Jami\’an Tsaro Sun Dira Gidan Tsohon Shugaban Kasa Namadi

0
2114

\"Anti-graft

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

WATA tawagar jami\’in hukumomin \’yan sandan ciki na DSS da Kuma jami\’an hukumar yaki da masu aikata laifukan da suka shafi kudi da cin hanci da karbar rashawa ICPC Sun yi dirar mikiya a gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, gidansa yana a lamba 1 ne kan titin Alimi cikin garin Kaduna.

Jami\’an sun isa katafaren gidan ne mai tsada mallakar tsohon mataimakin shugaban kasar \’yan mintoci kadan bayan karfe uku na ranar jiya, kuma suna cikin gidan har karfe biyar da rabi na yamma.
Kamar yadda majiyarmu ta bayyana mana jami\’an suna dauke da makamai ne masu nauyin gaske, sun kuma zo ne a cikin motoci uku, kirar Toyota Hilux da kuma mota mai bakin fenti kirar Toyota Corolla da kuma mota bas mai dirar mutane da yawa mai farin fenti.
Jami\’an dai wasu sun tsaya a waje suna jira wadansu kuma sun shiga daga ciki har suka kammala bincikensu baki daya.
Sai dai wakilinmu bai sami damar tattaunawa da jami\’i ko daya ba domin ya ji dalilin wannan ziyarar ba-za-ta ba a gidan na tsohon mataimakain shugaban Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here