Fiye Da \’Yan Boko-Haram Su 700 Ne Suka Mika Kansu Ga Hukumar Tsaro

0
673

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SAKAMAKON irin dagewar da jami\’an tsaron Nijeriya suka yi na yaki da \’yan Boko-Haram musmman wadanda suka makale a dajin Sambisa ya sa wadansu daga cikin su yin sarandar dole.
Kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojan Nijeriya babban hafsan soja Sani Usman Kuka-Sheka ya bayyana wa manema labarai cewa saboda irin yadda suke gudanar da aiki a dajin Sambisa ya sa tilas wadansu \’yan-ina-da-kisa da ke ta\’addaci dole suka yi saranda har 70 sun kawo kansu ga rundunar sojan kuma 700 su ma za su kawo kansu nan da dan kankanin lokaci.
\”Mun samu wadansu makamai ne masu nisan zango wadanda ake aiki da su, don haka shawara kawai shi ne su mika wuya domin ba aikin wasa ake yi\”.
Kamar yadda muka samu labari daga kafafen labarai cewa sojojin Nijeriya suna can sun dukufa wajen zakulo Abubakar Shekau a dajin Sambisa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here