AN FILLE KAN WASU MATASA 2 \’YAN UWA A JIHAR RIBAS

0
837
Daga Usman Nasidi
WASU da ba a san ko su wane ne ba, sun halaka da kuma fille kai na wasu \’yan\’uwa biyu, Ifeanyi da kuma Emeka Wobo, mazauna al’ummar Rumuokparali a karamar hukumar Obio Akpor da ke Jihar Ribas.
Jami’an ‘yan sandan jihar ne suka gano ragowar jikin \’yan\’uwan a kusa da Elekahia Housing Estate a Fatakwal babban birnin jihar a ranar Talata, 11 ga watan Yuli.
Majiyar ta samu labarin cewa \’yan\’uwan sun shiga wata motar kasuwa daga Rumuokparali a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli da yamma, kafin jami’an tsaro su gano gawawwakin su a washegari.
Shugaban matasan yankin, Mista Pamoses Omah ya shaida wa majiyarmu cewa labarin mutuwar ‘yan’uwan ya jawo hayaniya da kuma bacin rai a tsakanin al\’ummar yanki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here