Da Gaske Kayan Mata Sirrin Mallakar Miji Ne?

0
2427

Rabo Haladu  Daga Kaduna

KAYAN mata, ko ina ka duba sai kayan mata. Shin mene ne kayan mata? Wane amfani suke da shi? Me ya sa farin jininsu ya karu a \’yan shekarun nan?
Masana sun ce kayan matan hade-haden magunguna ne da ke samar da nishadi ga ma\’aurata. Akwai wani hasashen da ke cewa wadannan \’magungunan\’ ko hade-haden na iya saka maza cikin wani halin da ka iya mayar da su tamkar bayin matansu.
Amma kayan matan na da wani tasiri kuwa? Suna samar da wani amfani na ainihi?
A halin yanzu ba abin mamaki ba ne ka ga wata mai sayar da kayan mata a shafukan sada zumunta kamar Instagram tana tallata kayan, kuma abokan cinikinta na yabawa da \’tasirin kayan nata\’.
Da me a ke hada kayan mata? Me yasa suka bazu a ko ina? Anya suna aiki kuwa? Ko kuwa dabarun raba mata da kudadensu ne?
Akwai wata mai tallan kayan mata a shafin Instagram, wacce abokan cinikanta suke matukar yaba mata!
Na ga hoton wata mata a shafin nata tana cewa mijin matar wanda a ka shaide shi da mako, ya ba ta sabuwar mota har da wata jakar kawa ta miliyoyin naira!
Wannan kyautar ta biyo bayan da \’wai\’ ta yi amfani da wani hadin mai suna \’Karya Gado\’ ne. Wasu kuma na yabawa da kayan matan wajen \’hukunta\’ maza masu neman matan banza a waje.
Wasu matan kuma sun ce kayan matan na ba su damar mallake mazansu, don su rika yin dukkan abin da matan nasu ke so.
Labarin na da dadin ji; idan mace ta kurbi wani hadi, kawai kamar sihiri, sai mijinta ya zama tamkar wata tinkiya, ke kuwa kin zama wata sarauniya…
Daga nan kin mallake shi, kin kuma zame wata … Kina ganin kin cimma bukatunki ko? Kina ganin babu wani laifi tun da ai mijinki ne ko? Komai lafiya lau ko?
Amma akwai wani hanzari ba gudu ba, irin wadannan kayan matan na iya janyo wa matan da ke amfani da su matsalolin kiwon lafiya.
A cikin tattaunawar da muka yi da Dokta. Hauwa Musa Abdullahi, wacce kwararriyar likita cututtukan mata ce, ta fadakar da mu irin matsalolin da mata masu amfani da kayan mata ke fuskanta da suka hada da cututtukan
Ta kuma bayyana yadda hadin magunguna ke iya yin illa ga yadda farjin mata, ya barnata jikin matar, musamman irin wanda ake saka shi cikin jiki.
Likitoci na jan hankalin mata da su yi taka tsantsan wajen amfani da kayan mata. Saboda ma\’aikatan lafiya na ganin babu wani sahihin adadi na amfani da kayan.
Hajiya Aisha Ibrahim Isa, wacce aka fi sani da \’Aisha Gyara da kanki\’, ta shawarci mata su rika amfani da kayan mata a kodayaushe, domin suna inganta aurensu.
A ganinsu, dole ne mata su yi amfani da kayan mata idan suna son morar mijinsu.
Kuma suna ganin hakkin mata ce, ta \’iya rike\’ mijinta, domin ta kare shi da saduwa da matan waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here