Sun Nemi Da A Raba Kasar Nan Kowa Ya Kama Gabansa

0
772
Daga Usman Nasidi
YANZU haka kungiyoyin matasan nan na Arewa da suka ba Inyamurai wa\’adin barin yankin sun garzaya majalisar dinkin duniya domin neman taimako.
Gamayyar matasan a karkashin kungiyoyin yanzu haka sun aike wa da babban sakataren na majalisar dinkin duniya Antonio Guetarres da doguwar takarda mai shafuka 20 suna neman ya shiga maganar raba Najeriya.
Majiyarmu ta samu labarin cewa matasan na arewa a karkashin jagorancin Ambasada Shettima Yarima sun bukaci majalisar ta dinkin duniya da ta taimaka wa Najeriya wajen ganin an raba kasar an ba yankin na Inyamurai kasar su.
Haka kuma dai matasan a cikin takardar sun yi tir da kungiyar fafutukar neman yankin Biafra. Inda suka nuna bacin ransu a kan yadda shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ke ci gaba da yin tarurrukan rabewa duk da gargardin da kotu ta yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here