GWAMNAN LARDIN KASAR CHINA YA KAWO ZIYARA JIHAR KADUNA

0
670

Daga Usman Nasidi
GWAMNAN jihar Kaduna ya karbi bakoncin Gwamnan Lardin Habei na kasar Caina a karkashin jagorancin jakadan kasar Sin a Najeriya tare da shugaban kamfanin gine-gine na CCECC.
Wannan ziyara ta wakana ne fadar gwamnatin jihar Kaduna, gidan Sir Kashim Ibrahim, inda manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna da kwamishinoni suka halarci taron.
Jami’an kasar Cainan sun kawo ziyarar ne don rama bikin ziyarar da Gwamna El-Rufai ya kai musu a watan Mayu 2017, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.
A yayin ziyarar, jami’an gwamnatocin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar da suka shafi tattalin arziki, cinikayya, kasuwanci, gine-gine, al’adu, kimiyya da fasaha, Ilimi, kiwon lafiya da kuma yawon bude ido.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here