AN TSINCI GAWAR YARA 3 DA AKE ZARGIN AN KASHE SU A WATA MOTAR MAKWABCIN GIDANSU

0
752

RUNDUNAR \’yan sanda tana bincike a kan gawar wadansu yara uku \’yan gida daya da aka tsinta a cikin wata mota a jihar Kaduna.

A can jihar Kaduna ne aka tsinci gawar wasu yara guda uku \’yan gida daya a cikin wata mota, inda har yanzu ake binkicen sanadiyyar mutuwar tasu.
Rahotanni sun bayyana cewa, iyayen yaran wadanda mazauna unguwar Tudun Wada ne a jihar ta Kaduna sun bayyana cewa, tun a ranar Larabar makon da ya gabata ne suka nemi yaransu guda hudu suka rasa inda suke kasa ne ko sama .
Wani daga cikin mahaifin yara biyu daga ciki, Suleiman Hashim, ya bayyana cewa kwanaki uku suka yi wajen neman wadannan yara; Hamza, Ikram,Ilham da Raihan wanda duk cikin su babu wanda ya haura shekaru uku da haihuwa.
Sai a ranar Asabar ne suka tsinci gawar wannan yara a cikin wata motar makwabcinsu duk sun rasu in ban da Ilham, wadda a halin yanzu tana karbar kyakkyawar kulawa a asibiti.
Rundunar \’yan sanda ta jihar suna nan a bakin aiki don gano sandiyyar mutuwar wannan yara don tsananta bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here