Kashi 95 Cikin 100 Na \’Yan Ta\’adda A Dazukan Arewa Ba Fulani Ba Ne – Gwamna Masari

0
1057

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNAN Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya fito fili karara ya bayyana cewa suna da masaniyar shigowar \’yan ta\’adda cikin dazuzzukan da ke kewaye da jihohinsu.
Ya kuma bayyana cewa a bisa irin yadda suka gudanar da aikin tabbatar da tsaro wanda ya ba su damar samun masaniyar gano cewa kashi casa\’in da biyar cikin dari na Fulanin da ke cikin dazuzzuka ba \’yan ta\’adda ba ne, wasu ne kawai da suka fito daga wani wuri amma ba ainihin mazaunan yankin ba.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Masari, ya ce za kuma su tabbatar kwamitin da aka kafa a taron gwamnoni ya samu nasarar samun bukatar fayyace wa jama\’a me ake nufi da batun sake fasalin kasa domin cimma nasarar da kowa ke bukatar samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here