AMBALIYAR RUWA TA HALLAKA MUTUM 10 TARE DA LALATA GIDAJE 1,153 A JIHAR FILATO  

0
622

 Isah Ahmed, Jos

DAGA watan mayu zuwa watan yunin da ya gabata, ambaliyar ruwan sama ta hallaka mutum 10 tare da lalata gidaje  1,153 a jihar Filato.

Sakataren hukumar agajin gaggawa ta jihar, Alhaji Alhassan Barde ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos babban birnin jihar Filato.

Ya ce kananan hukumomin jihar Filato  da wannan ambaliyar ruwa ta shafa sun hada da Jos ta Arewa da Jos ta kudu da Bokkos da Kanke da Wase da Shendam da Mikang da Jos ta gabas da Langtang ta arewa da kuma  Langtang ta kudu.

Sakataren ya yi bayanin cewa hukumar agajin gaggawa ta jihar Filato tana yin iyakar kokarin ta wajen ganin ta tallafawa wadanda wannan al’amari ya shafa.

‘’A watan mayu  da ya gabata mun gano cewa ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 10 tare da lalata gidaje  1,153. Wannan ambaliyar ruwan sama ta lalata kauyuka guda 832 a dukkan kananan hukumomin jihar Filato  17.’’

Ya ce nan bada dadewa ba zamu shiga dukkan kananan hukumomin da wannan annoba ta shafa, domin gane wa idanunmu halin da wadanda wannan annoba ta shafa suke ciki. Kuma mu ji irin abubuwan da suke buqata domin zo mu sami gwamnatin jihar Filato a san yadda za a yi a tallafa masu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here