Sun Karrama Shugaban Kasuwar Potiskum

0
1195
Muhammad Sani  Chinade, DAGA DAMATURU
A kwanakin baya ne dai kungiyar \’yan kasuwa da ke babbar kasuwar garin
Potiskum a Jahar Yobe suka gudanar da bikin karrama  sabon shugabansu
na riko Alhaji Isa Sakatare saboda jin dadin irin shugabancin da yake
gudanarwa da suka dade ba su ga irin ya hakan ba tun kafa kungiyar sama
da shekaru 40 da suka gabata.
Wannan biki na karrama shugaban  kungiyar an gudanar da shi ne a
gidan sinima na Muhammad Idris da ke tsohuwar kasuwar Potiskum tare da
samun halartar manya-manyan mutanen da suka hada da wakilan masu
martaba sarkin Fika da sarkin Potiskum da Mai Tikau  da Mai Gudi sai
kuma Madakin Tikau Alhaji Musa Lawan da shugaban
kungiyar \’yan kasuwar Damaturu Alhaji Garba Bazam da sauransu.
Da yake jawabi sabon shugaban Alhaji Isa Sakatare ya ce lokacin
da ya karbi rikon shugabancin kungiyar kasa da shekara guda ya zana
muhimman kudirorinsa guda 7 da suka hada da bukatar dogaro da kai da kokarin kare dukiyar \’yan kasuwar wadda a kan haka sai da ya samar da dokar bude kasuwar daga karfe 6.00 na safe tare da rufeta da karfe 7.30 na yammacin kowace rana. Kana ya samar
da sahihan masu gadin kasuwar karkashin Sarkin \’Baka\’ wadanda ake
biyansu albashin Naira dubu 10 a duk wata kowannensu.
Ya kara da cewar a yanzu haka ya sa an samar kofofi manya-manya ga
kofofin shiga kasuwar don kara karfi ga harkar tsaron dukiyoyin \’yan
kasuwar. Haka nan a cewarsa ya yi yunkuri da taimakon Allah (SWT) da
kuma taimakon shugaban riko na karamar hukumar Potiskum Alhaji
Muhammad Musa an samar da tashar kashe gobara a kasuwar.
Alhali Isa Sakatare ya kara da cewar,a yanzu haka ya kafa kwamitoci
daban-daban guda 9 da za suke gudanar ayyuka don habaka kasuwar ta
Potiskum. Kana a halin yanzu daga \’yan watannin da ya yi a kan
jagorancin kungiyar tunin ya sayi motoci guda biyu ga kungiyar daya
motar tifa daya kuma motar sharon duk da kudaden da kwamitinsu na riko
ya tattara a dan lokacin da suka yi.
Daga nan sai ya nemi mambobinsu da su ci gaba da addu\’ar daurewar ci
gaban kasuwar domin a cewarsa harkar kasuwanci shike jan akalar
tattalin arzikin manyan kasashen duniya da suka ci gaba. Kana ya
kirayi \’yan kasuwar da a ci gaba da addu\’ar neman zaman lafiya domin sai da zaman
lafiya ne za a samu damar gudanar da harkokin kasuwancin kansa.
Da ya ke jawabi Madakin Tikau Alhaji Musa Lawan ya gargadi \’yan
kasuwar ne da su yi hattara kan harkokinsu na kasuwanci domin kuwa
akwai bukatar su sa Allah gaba tare da guje wa tsawwala farashin da ya
wuce domin yin hakan ne ke haifar da yawancin bala\’in da ke afka wa
kasuwanni. Kana ya yaba wa wannan shugaban \’yan kasuwa dangane da
ayyukan ci gaba da ya gudanar a kasuwar.
Madakin na Tikau ya ci gaba da cewar in har ci gaba ake nema to lalle
a yanzu an samu shugaba wadda ke bukatar su kokarta ci gaba da sa shi
gaba don shugabantar kungiyar na tsawon lokaci.
Kungiyar dai ta karrama mutane sama da 19 da lambar girmamawa daga kowane
bangare na kasuwanci har da wasu mashahuran mutanen da suka rigamu
gidan gaskiya wadanda kafin rasuwarsu sun bada gagarumar gudummawa ga
ci gaban kasuwancin garin da suka hada marigayi Alhali Yaro Gambo da
Alhaji Barau (ABC) da sauransu.
Bayan tashi a taron ne wakilinmu ya samu tattaunawa da wasu mambobin
kungiyar kamar Alhaji Gambo mai citta yadda ya ce ai su babu abin da
za su cewa wannan shugaba nasu sai fatan alheri domin a cewarsa a da
duk karshen wata dubu 2 ya ke bayarwa kudin kasuwa amma tun daga hawan
wannan shugaba ba\’a taba zuwa an tambaya ko kwandala ba.
Shi kuwa Alhaji Umaru mai manja cewa ya yi shi a iya saninsa kungiyar
\’yan kasuwar Potiskum ba su taba samun shugaba mai hangen nesa da
tsayin daka don ciyar da kungiyarsu gaba irin wannan shugaban riko na
su. Don haka a cewarsa \’\’Tazarce\’\’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here