GWAMNATIN JIHAR KADUNA ZA TA SAMAR DA KUJERU 256,182 A MAKARANTUNTA

0
678
Daga Usman Nasidi
GWAMNATIN Jihar Kaduna ta ba da kwangila don samar da isashen kujerun zama a makarantu, kwamishinan Ilimi a jihar, Farfesa Andrew Nok ya tabbatar da hakan.
Kwamishinan ya ce wannan shirin zai taimaka wajen inganta ilimi da ilmantarwa a makarantun gwamnati.
A kiyasin da aka zayyana a wata takardar da aka gabatarwa manema labarai a ranar Talata, 8 ga watan Agusta ta nuna cewa gwamnatin jihar ta ba da kwangila don samar da kujeru 186,182 a karkashin wani shirin gaggawa na gwamnatin jihar wanda aka sani da education emergency intervention programme.
Majiyarmu ta tabbatar da cewar, bisa ga wannan takardun, an samar da kujeru 167,982 ga makarantun firamare da kuma 18,200 ga makarantun sakandare.
Ya kara da cewa an bayar da wani kwangila domin samar da karin kujeru 70,000 wanda zai kawo yawan kujeru da ake tsammani zuwa 256,182.
Nok, yayin da yake karbar wasu kujeru 700 a makarantar sakandaren Government Day Secondary School, sabon tasha a Kaduna, ya ce har zuwa yanzu an ba da kujera 90,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here