SHUGABAN MASU SANA\’AR SAYAR DA KARO A JAHAR YOBE YA KOKA KAN YADDA SANA\’AR TASU KE FUSKANT

  0
  635
  Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
  SHUGABAN kungiyar masu sana\’ar sayar da karo na Jihar Yobe Alhaji Mele
  mai karo Damaturu ya koka dangane da yadda sana\’arsu ke fuskantar
  barazanar bacewarta sakamakon yawaitar sare bishiyoyin da ke
  samar da karo da ake yi don neman itacen girki.
  Shugaban ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakilinmu a garin
  Damaturu dangane da matsalolin da wannan sana\’a tasu ke fuskanta.
  Alhaji Mele ya kara da cewar, a baya kafin mutane su farma saran
  itatuwan karo a duk mako sukan loda manyan motoci fiye da biyu  da
  karo amma a halin da ake saboda karancinsa da kyar suke loda mota daya
  a mako duk da irin darajarsa a kasuwannin duniya da yake da ita.
  Don haka ne ya ke rokon gwamnatin Jihar Yobe da ma sauran gwamnatocin
  sauran Jahohin da ake samar da karo da su kara daukar matakin dakatar
  da sare itatuwan karo da wasu mutanen da ke sana\’ar saran itatuwa
  barkatai ke yi domin matukar ba hakan aka yi ba to nan gaba wannan
  sana\’a kan iya gagararsu.
  Ya  kuma roki gwamnatin tarayya da ta sa su cikin shirin da take yi na
  tallafa wa manoma da kudaden gudanar da noma ko da ma rance ne domin
  kuwa suma wani bangare ne daga sashin manoma.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here