ALHAZAN FILATO 400 NA SHEKARA TA 2014 ZA SU TAFI AIKIN HAJJIN BANA

0
661

 Isah Ahmed, Jos

GWAMNATIN Jihar Filato ta bayar da umarni ga alhazan jihar  guda 400 da suka biya kudadensu a shekara ta 2014, amma basu sami tafiya aikin hajjin ba, su zo su cika kudaden kujerar su idan suna bukatar tafiya aikin hajjin bana. Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar  kuma Amirul hajjin bana na jihar Alhaji Yusuf Dayyabu Garga ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida kan shirye shiryen aikin hajjin bana na jihar Filato a garin Jos.

Ya ce gaskiyar magana ita ce a shekara ta 2014 akwai alhazan jihar  da suka biya kudadensu, amma ba su sami tafiya ba. Kuma  da wannan gwamnati ta zo ta yi bincike kan maganar ta  gano cewa an karbi kudaden alhazan,   an ba su rasidai  amma  babu kudaden a asusun gwamnatin jihar.

‘’Ya zuwa yanzu hukumomin EFCC da ICPC suna nan suna bincike kan wannan al’amari.

 Don haka gwamnatin jihar ta tausayawa wadannan alhazai ta ba da umarnin dukkan alhajin da yake da ikon cika kudin ya cika, idan kuma mutum ba shi da ikon cikawa za a bashi kudin da ya bayar tun da farko. Ya ce sakamakon wannan dama da aka basu, da dama sun cika kudin zasu tafi aikin hajjin bana, wasu kadan ne basu cika ba,  zasu  jira da zarar an tafi aikin hajji da kwana biyar, za a basu kudaden da suka biya tun da farko’’.

Ya ce a bana an bai wa jihar Filato kujeru 1400  amma ya zuwa wannan lokaci alhazai 1128  ne aka tantance za su tafi aikin hajji daga jihar.

Alhaji Dayyabu Garga ya yi bayanin cewa  tuni an tantance alhazan, malamai sun yi masu  bita kan aikin hajjin. Kuma a ran alhazan Filato za su fara tashi ne a ranar 21 ga wannan wata.  Ya ce a wannan shekarar alhazan jihar Filato za su tashi daga Bauchi ne, sabanin Kaduna da aka saba tashi a kowace shekara.

Ya yi kira ga alhazan jihar Filato  idan sun isa kasa mai tsarki, su tabbatar sun yiwa kasar nan addu’a da shugaban kasa Muhammad Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here