CAJIN WAYA YA YI MINI GOMA-TA-ARZIKI–IBRAHIM MAI AKUYA

  0
  903
  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga  kalaba
  TUN daga lokacin da wayar tafi-da-gidanka wato wayar salula ta shigo
  Nijeriya aka kafa sana\’ar rika cajin batirin wayar wani lokaci ma har
  ma da wayar kamar wasa wannan sana\’a wadanda suke yinta suna kara
  karuwa wannan ne ya sanya wanda ya fara kafata a Kalaba Jihar Kuros
  Riba Alhaji Ibrahim Isah wanda aka fi sani da Alhaji Ibrahim Mai Akuya
  shugaban kungiyar na Kuros Riba a hira da wakilinmu na kudanci ya
  tabbatar wa makaranta jaridar Gaskiyatafikwabo cewa bayan rufin asiri
  da take ga mai yinta sai dai fa akwai \’yan matsaloli da wasu mutane
  abokan ma\’ala kan haddasa amma sun dauki mataki.
  Ga yadda hirar ta kasance:-
  GTK: Gabatar wa makaranta wannan jarida sunan ka?
  Ibrahim Mai Akuya: Sunana Alhaji Ibrahim Isah
  GTK: Ya sunan wannan kungiya taku?
  Ibrahim Mai Akuya: Sunanta kungiyar masu saye da sayar da kayan waya
  wato wayar salula ko wayar tafi da gidanka kamar yadda wasu ke
  kiranta.Kuma anan Kuros Riba ina xaya daga cikin wanda ya fara wannan
  sana,a kuma ya kafata har ya assasata .nine na fara yin harkar waya
  anan layin bagobiri ,unguwar hausawa.
  GTK: Wace shawara kuka yanke har ma kuka kafa wannan kungiya ganin cewa
  a wasu lokuta idan anma kafa kungiya ba kasafai take dorewa ba saboda
  wasu dalilai na cikinta?
  Ibrahim Mai Akuya:Abin da ya sa muka kafa wannan kungiya saboda
  matsaloli da suke shigowa ciki,saboda yau za a iya cewa an kawo wa
  mutum cajin waya shi bai sani ba ashe sato waya aka yi aka kawo masa
  caji to shine muka tantance muna da kati duk wanda ya zo ya kawo cajin
  wayarsa ko ta batirin waya sai mu ba shi wannan kati mu rubuta lambar
  katin a jikin wayar ko kuma batirin yadda idan ya zo karba sai ya kawo
  mana katin sannan mu kuma mu ba mutum wayarsa ko kuma batirinsa da ya
  kawo caji.
  GTK : Ka yi zargin cewa bata gari ne da suka yi yawa yasa daya daga cikin
  dalilan da suka sanya kuka kafa wannan kungiya, a cikin abokan sana\’a ce
  ko ta hulda suke kawo maku matsala?
  Ibrahim Mai Akuya: ba a abokan sana\’a ba ne ba kuma ta hulda ba ne
  ,saboda wani idan ya tashi zuwar maka zai zo maka a kammalallen mutum
  cikin kamala da komai ya kawo maka waya caji amma ba za ka taba sanin
  wayar nan da ya  kawo maka caji sato ta aka yi ba , masu gyara suna
  shiga matsala mu da muke yin caji muna shiga matsala.
  GTK: Wannan mataki da kuka dauka na kare mutuncin ku dana sana,ark u
  kwalliya na biyan kudin sabulunta?
  Ibrahim Mai Akuya: Insha Allahu idan ma muka ba mutum kati ya jefar a
  matsayin ya jefar da wayarsa ko kuma batirinsa yake.
  GTK: Ka ce kai ne ka kafa wannan sana,a a nan kuros riba shin daga
  lokacin zuwa yanzu ko an samu cimma wata buka ?
  Ibrahim Mai Akuya: Alhamdulillahi gaskiya magana da gaskiya akwai
  rufin asiri akwai kuma  cimma biyan bukata saboda idan dai mutum yana
  wannan sana\’a zai iya  rike kansa ya iya rike iyalansa ba sai ya je
  ya yi \’yar murya ba wani ya taimaka masa ba da  abinda zai je ya ci
  abinci ba.
  GTK: Kamar akwai bukatar babban jari a yi tanadi ga mai son kafa wannan sana\’a ?
  Ibrahim Mai Akuya:Eh! Ita gaskiya abin da take so ba wani dogon jari
  bane mai karfi sosai tana bukatar janareto,tana bukatar abubuwan da
  ake hada kayan cajin sannan idan sana\’ar ta bunkasa kuma sai ka rika
  sawo kayan waya kana zuwa kana sayarwa  kayan asosaris saboda wata
  rana za a iya zuwa a tambayeka iyafis ko batir ko gidan waya .
  GTK: Ko kungiyar ku ko ta taba neman taimako daga gwamnatin jiha domin
  bunkasa wannan sana\’a tun da ka ce ka rike mukami a matakina kasa reshen
  jihar Kano?
  Ibrahim Mai Akuya:Eh! Bana mantawa magana ta gaskiya lokacin da malam
  Ibrahim Shekarau yake gwamnan kano ya taba zuwa nan Kuros Riba ya turo
  makarrabansa sun bayyana ra,ayin su da irin sana\’ar da suke yi sun
  nuna za su taimaka a  lokacin amma har yanzu babu abin da aka yi.
  GTK: Wane irin kalubale kuke fuskanta a wannan sana\’a?
  Ibrahim Mai Akuya:To kalubale da muke fuskanta za ka zo mutum batirinsa
  ya bata ko cajarsa kaga mutum y na surutu da sauran su idan aka samu
  mai caji yana da tawakali shima wanda ya kawo cajin yana da tawakali
  sai ka ga an daidaita an yi sulhu ko mai caji ya biya kudin ko kuma mai
  kayan ya dauki kaddara ya hakura.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here