RASHIN SAMAR DA TAKIN ZAMANI A DAMINAR BANA YA JAWO KOMA BAYA GA HARKOKIN NOMA A JIHAR Y

0
646
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
RASHIN samar da takin zamani ya jawo mana koma baya matuka ga harkokin
mu na noma a daminar bana a kusan dukan yankin mu na karamar hukumar
Jakusko da ma jahar Yobe baki daya.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Alhaji Hamisu Sarkin noman
Marcha a tattaunawarsa da wakilinm0 dangane da yadda manoma ke ji na
rashin samar musu da takin zamani a daminar bana.
Alhaji Hamisu sarkin noma ya kara da cewar sun dade rabonsu da samun
kansu cikin irin wannan hali na faduwar hannu ga harkokinsu na noma
illa wani bangare na amfanin gona kamar shinkafa da aka dan sameta a
wadace wadda kuwa ba komai ya haifar musu da hakan ba sai ganin irin
yadda a bana gwamnatin Jahar ta gaza samar musu da takin zamanin da za
su zuba a gonakensu don amfanin gonarsu aksari sun yi sanyi ta yadda
in ba an zuba musu takin zamanin ba, ba su cika samar da amfanin gona
mai yawa ba.
Ya kara da cewar a duk shekara ta bangarensa ya kan noma fiye da
buhuna 100 na gero da dawa to amma a bana bai yi tsammanin zai samu
bubu 20 ba. To ai kaga an samu matsala babba tunda a gidansa kadai ya
kan ci kamar buhuna 50 na abinci a duk shekara.
Sarkin noman ya ci gaba da cewar, kowa ya san halin da su manoman
Jahar Yobe suka yi fama da shi a baya na rashin kwanciyar hankali
sakamakon take-taken
marikitan Boko Haram, to yanzu da wacce za su ji? Za su ji da kokarin
mayar da irin barnar da aka musu ko da fafutukar ciyar da kan su tunda
amfanin gonar da suke sa ran nomawa ba ba su yi tsammani  zai iya kai
yawan yadda zai rike su ba saboda rashin taki in dai ba Allah SWT ba
ne ya kawo musu dauki.
Don haka a cewarsa manoman jahar Yobe na ganin gwamnatinsu na shirin
taka rawa na halin da za su iya samun kansu na rashin samar
musu da takin zamanin da za su zuba a gonakensu tunda in da an samar
musu takin da za su iya samun yalwar abinci tunda Allah (SWT) ya
saukar da ruwan sama mai yawa a daminar ta bana.
Daga nan sai ya roki gwamnatin da ta yiwa Allah in Allah (SWT) Ya kai
rai badi ta kokarta ta samar wa manoma taki akan lokaci ba sai lokaci
ya kure ba.
To sai dai wata majiyar ta asirtawa wakilinmu cewar gwamnatin Jihar ta
ware zunzurutun kudi kusan Naira Miliyan 199 don samarwa manoman Jihar
takin zamani da kusan kudinsu ya tasamma tirela 53 a wannan damina ta
2017 wadda majiyar ta tabbatar da an samar da takin amma kuma duk da
hakan talakawan na korafin rashin samun takin a wadace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here