An Hana Sayar Da Ragunan Layya A Titunan Jihar Neja

0
860

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SAKAMAKON irin yadda haifar da cinkoso da cinikayya barkatai ke haifar da samar da matsalar tsaron dukiya da rayukan jama\’a yasa Gwamnatin Jihar Neja ta Arewacin Nijeriya ta haramta dukkan saye da sayarwar raguna a bakin titua da wadansu ma\’aikatun gwamnatin jihar baki daya.
Kamar dai yadda aka sani a duk lokacin babbar sallah wato sallar layya wadansu \’yan kasuwa da ke sayar da raguna na cika gefen tituna da kuma harabar wasu ma\’aikatun gwamnatin musamman a babban birnin jihar suna kokarin saye da sayarwa.
Kamar yadda gwamnatin Neja ta bayyana cewa saboda hakan za a iya samar da matsalar tsaro da kuma kazanta iri daban-daban.
Gwamnatin ta bayyana wani katon katafaren filin da ke kusa da kasuwar Kure da cewa nan ne aka amince a yi hada-hadar raguna ta bana.
A ta bakin shugaban kungiyar masu sana\’ar sayar da dabbobi a jihar sun bayar da sanarwar cewa dukkan wadanda za su kawo raguna lallai su guji daure dabbobi a wuraren da ba a amince ba kuma su sani cewa ba su da hannu a cikin karya wannan doka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here