An Yanke Makin Da Za A Shiga Jami\’o\’in Tarayyar Najeriya

0
738

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MINISTAN kula da ilimi na kasa Malam Adamu Adamu ya bayyana jadawalin yawan makin da dalibai za su samu bayan sun rubuta jarabawar shiga jami\’a wato (JAMB) da kuma kudin da dalibai za su biya idan suna son rubuta jarabawar shiga jami\’a da ake shiryawa ana rubutawa a jami\’o\’in.
Kamar dai yadda aka sani ga duk dalibin da ke son shiga jami\’a ta hanyar hukumar (JAMB) dole a yanzu ya samu maki akalla 120 sai kuma maki 100 ga masu son shiga kwalejin kimiyya da fasaha sai maki 110 ga masu son shiga kwalejin koyon sana\’o\’i .
Batun kudin da dalibai za su biya kuma domin rubuta jarabawar jami\’o\’i da ake ce wa Post Ume kuma kada kowace jami\’a ta karbi kudin da suka gaza dubu biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here