GWAMNA EL-RUFA\’I YA GARGADI JAMA\’A DASU DAINA YADA JITA-JITA

0
687
Daga Usman Nasidi
GWAMNA Nasir El-Rufa\’i na Jihar Kaduna ya ja kunnen al’umman jihar da su daina yada rade-radi da ka iya tada zaune tsaye a jihar musamman a karamar hukumar Kajuru da sauran sassan jihar.
Sannan kuma ya bukaci mutane da su daina amfani da shafukan zumunta musamman Facebook wajen yada hotunan da ka iya tada rikici a jihar.
Da yake jawabi mai magana yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan a wata takarda da sanya ma taken El-Rufai ya ce duk mutumin da aka kama da laifin haka zai fuskanci hukunci.
Akalla mutanen 33 suka rasa rayukansu a rikicin Kajuru wanda mafi yawansu Fulani ne.
Gwamnatin ta ba Jami’an tsaro a jihar damar kamo wadanda ake zargin da rura wutan rikici a jihar.
Gwamnatin ta da tabbacin cewa lallai za ta hukunta duk wanda ta samu yana da hannu a rikicin da ya faru a karamar hukumar Kajuru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here