Gwamna Masari Ka Farka Daga Gyangyadin Da Kake Yi

  0
  967

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Funtuwa

  KAMAR yadda gwamnatin APC karkashin Muhammadu Buhari da a Jihar Katsina Honarabul Aminu Bello Masari duk suke da taken canji, ya dace Masari ya kalli wannan lamarin idan ya yi kitso da kwarkwata sai ya hanzarta magancewa.
  Wannan batun dai na neman a ba shi kulawa ta musamman ba a rika tafiya kamar irin ta shekarun da suke wuce can baya ba, ga duk wanda ya san garin Funtuwa kowa ya sani babban wuri ne da ya kai kololuwar ci gaba idan an yi duba a Nijeriya, domin gari ne na noma, kiwo da masana\’antu da ya tabbata ko kasancewa wurin zama santa (tsakiya ) babba.
  Amma dalilin cewa canji shi ne za ka ga a garin Funtuwa akwai ofisoshin jami\’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa, ofishin VIO da ofishin masu aikin tara kudin haraji na jiha da na tarayya amma duk da wadannan a garin Funtuwa akalla za ka iya ganin baburan haya da na kawa kawai ba tare da an yi haya na akalla dari biyar, kuma duk babu mai dauke da lamba.
  A Jihar Katsina ne za ka ga mutum ya sayi babur har ya kashe shi amma ba zai yi masa lamba ba kuma ana hawa kan titin gwamnati da shi, shin ina canji a nan?
  Kuma ina batun tara kudin shiga ga jiha? Haba Masari na fa ji a wasu jihohi ana cewa, gwamnatin jiha ce ke da alhakin sayowa da sayar da lamba ko jihar Katsina ba ta san yadda za ta tattara kudin shiga ba ne?
  KITSO DA KWARKWATA
  Shin ko Masari ya san irin mutanen da ya nada a wannan bangare na tara haraji da na masu ikon kula da ababen hawa har da lamba a ciki, shin ko dai akwai lauje cikin nadi ne da gwamnan bai sani ba?
  TSARO
  Akwai wani al\’amarin da ke addabar masu haya da babura a garin Funtuwa da sauran yankunan shi ne na barayin babura, wanda sanin kowa ne ko a watan Azumin da ya gabata sai da aka samu matsalar hakan, saura kiris a samu tashin hankali a Funtuwa inda wasu \’yan achaba suka yi kokarin kona wani barawon babur,wanda har sai da aka kawo karin jami\’an tsaron kwantar da tarzoma. Shin ina batun lamba ga babura ko lambar ba ta cikin tsari ne ko ma uwa-uba ta taimaka wa harkar tsaron ababen hawa.
  \’YAN ACHABA DA MASU BABURA
  Na samu zantawa da wasu masu sana\’ar haya da babura inda suka yi kokarin gaya mini sun fi dubu da ba su da lamba a garin Funtuwa da kewaye.
  Su ma masu abin hawa na babura sun shaida min cewa, ta yaya mutum zai sayi babur ya kuma tsaya yin lamba haka kawai?
  Dan wannan da kuma wasu binciken samun kudin haraji duk mun bincika mun samo za mu kawo su nan gaba
  AIKIN GINA TASHAR FUNTUWA
  Hakika aikin ginin tashar Funtuwa lamari ne a ke neman zama tamkar abin dariya domin ya zama abin magana da gori ga \’ya\’yan APC na yankin.
  Kuma kasancewar garin Funtuwa babban birnin da ko Katsina ta san da haka wajen yawan jama\’a, haraji da ci gaba a yanzu dai babu wata takamaimiyar tashar mota ,ko ina sukuwa ake yi da daukar fasinja,  abin da ke kawo cikas ga haraji fatan kungiyar NURTW sauran su.
  MASU AIKIN SHARAR TITUNA
  Lamarin rashin tasha na haifar wa da masu aikin sharar tituna musamman babban titi matsalar kasa yin aiki cikin lokaci da kuma kwashe sharar, domin a wasu wuraren motoci da masu kasuwanci suka mamaye wuraren tsawon lokaci.
  Don haka jama\’a na cewa ko domin a samu kudin shiga ta hanyar yin lamba da kuma tsaron ababen hawa, ya dace gwamnatin Masari ta dauki mataki.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here