Da Alamu Raguna Za Su Yi Kwantai A Kasar Nan Bana

  0
  759

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  A daidai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 4 a gudanar da bukukuwan babbar sallah, raguna na nan jibge a kasuwanni babu masu siya .
  A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayan raguna da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwa ba har zuwa yanzu.
  Masu sayar da dabbobi a kasuwanni sun ce, duk da kudaden ragunan sun banbanta da na bara ,ba a zuwa ana saya sosai.
  Masu siyan ragunan da yanzu suka siya, sun shaida wa  manema labarai cewa, farashin ragunan a bana da sauki idan aka kwatanta da na bara.
  A bara dai-dai sai da aka kai raguna sayarwa a kasuwanin Jamhuriyar Nijar daga Najeriya sanadiyar tabarbarewar darajar da Naira ta yi.
  Tambayar ita ce, shin ko a bana ma saboda rashin cinkin raguna yayin da Sallah ke karatowa zai sa \’yan kasuwa fita da ragunan nasu zuwa kasashen waje makwabta?

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here