Ya Tura Mahaifinsa Da ‘Yan Uwansa Don Tsafi Da Su Ta Hanyar Facebook

0
810

MUSA  MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

WANI matashi da ‘yan sanda a Jihar Anambra suka  cafke  dan shekara  26 da haihuwa mai suna Chukwuemeka Okafor e ya yi amfani da shafin sada zumunta na face book domin ya halaka mahaifinsa da kannensa biyu  tare da wasu abokansa biyar da ya hada ya sanya hotunansu a shafinsa kamar yadda ya sanar wa ‘yan sanda.Ya ce ya sa kokarin bayar da mahaifinsa ‘yan uwansa biyu  ya  hada baki da wasu abokansa su biyar  domin mika mutanen wajen boka .

Wannan lamari ya faru a kauyen Ifite-Awka da ke jihar Anambra ,wanda ake zargi Chukwuemeka  kafin asirinsa ya tonu sai da ya lallabi mahaifinsa ya ba shi  N100,000  da nufin zai yi kasuwanci karshe sai ya buge da tarewa wajen bokaye ya bayar da sunan mahaifinsa da,kannensa,lokacin da  abokan sa suka raka shi.

Okafor ya bayyana wa ‘yan sanda da bakinsa ba tilasta masa suka yi ba cewa  ya tsinci kansa cikin wannan hali ne bayan da wani abokin huldar kasuwancinsa ya damfare shi   kudi nair 400 da nufin za su tafi kasar Dubai kasuwanci karshe ya nemi abokin kasa ko sama .inji shi

Daga baya “na je na samu wani abokina kuma mai suna Zaki na fada masa damuwata na ce  ina cikin matsala shi kuma ya ce min idan ina son yin arziki dare daya dole ga sharuda amma fa kada in kuskura fada wa kowa sirrin idan na fada  zan mutu don haka sai ya ce mu kulla hulda ta shafin sada zumunta  na face book daga nan sai na sanya hoton babana da na kannena a shafina “.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da wanda ake zargin chukwuemeka Okafor ,kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra Garba Umar ya ce “a bayanin da mailifin da ake zargi ya yi ya ce hakika ya aikata laifin kuma mahaifinsa bai san cewa wadancan kudi da ya  bayar  ya ba boka ne domin a kashe shi ba. tare da sauran abokansa biyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here