GWAMANATIN BUHARI TA KARE DARAJAR AMFANIN GONAR DA MANOMA SUKA NOMA A BANA- FARFESA DADARI

0
744
Isah Ahmed, Jos
WANI masani kan harkokin noma a Nijeriya  kuma malami a sashin
binciken aikin gona da ke jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya Farfesa
Salihu Adamu Dadari ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari ya
taimaki manoman kasar nan, ya kare masu darajar dinbin kayayyakin
amfanin gonar da suka noma a daminar bana. Farfesa Salihu Adamu Dadari
ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce a bana Allah ya baiwa talakawa Nijeriya ikon yin noma mai tarin
yawa kuma  ya saukar da ruwan sama wadatacce, don haka manoma sun  yi
noman shinkafa da masara da sauran kayayyakin amfanin gona fiye da
kowace shekara.
Ya ce yanzu manoman Nijeriya suna son gwamnati ta ba su kariya na ganin
sun sayar da amfanin gonar da suka noma da daraja.
‘’Gwamnati ta kafa kasuwannin sayen kayayyakin amfanin gona masu tsari
wadanda za su sayi kayayyakin amfanin gonar da manoma suka noma a bana.
Kuma ta sanya farashi kan kayayyakin amfanin gonar da manoma suka noma
a bana, kuma  ta fito da kudi ta sayi rarar amfanin gona da manoma
suka noma ta adana a rumbunanta. Kuma matukar shugaban kasa yana son
Nijeriya ta tsaya a matsayinta na ci gaba da aikin noma a rika aikawa da
kayayyakin amfanin gonar da aka noma a Nijeriya zuwa kasashen waje.
Domin manoman Nijeriya su ji dadi, tattalin arzikin Nijeriya ya
farfado’’.
Har ila yau  ya yi kira ga shugaban kasa ya dakatar da maganar
masarar nan da ake cewa an shigo da ita daga kasashen waje. Saboda
wannan abu zai jefa manoma cikin bala’i kuma  zai rushe alkawarin da
gwamnatin Buhari ta yi wa mutanen Nijeriya na bunkasa harkokin noma a
Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here