SANATA HUNKUYI YA RABA BABURA DA KEKUNAN DINKI A KARAMAR HUKUMAR LERE

  0
  857
  Isah  Ahmed, Jos
  SANATA mai wakiltar mazabar zone 1 da ke Jihar Kaduna Sanata Sulaiman
  Usman Hunkuyi ya raba wa ‘yan siyasa baburan hawa da kekunan dinki da
  injinan ban ruwa a karamar hukumar Lere da ke mazabarsa.
  Da yake  jawabi a wajen raba wadannan kayayyaki, Sanata Sulaiman Usman
  Hunkuyi ya bayyana cewa baburan hawa guda 25 da kekunan dinki guda 45
  da injinan ban ruwa guda 45 da aka raba, an yi haka ne domin a
  tallafa wa jama’a su sami sana’o’in da za su rike kansu.
  Sanatan wanda daraktan yakin neman zabensa Honarabul Abubakar Umar
  Yariman Bomo ya wakilta ya yi bayanin cewa wannan rabon kayayyaki da
  aka yi kashi na farko ne. Ya ce nan gaba za a sake rabon kayayyakin
  kashi na biyu da kashi na uku.
  Ya yi kira ga wadanda suka sami wadannan kayayyaki su gode wa Allah
  kuma su yi amfani da su kamar yadda ya kamata.
  A nasa jawabin Ko’odinatan Sanatan a karamar hukumar Lere Murtala Sani
  Maskawa ya bayyana cewa kafin wannan rabon kayayyaki, Sanata Sulaiman
  Hunkuyi ya samar wa  ‘yan wannan karamar hukuma ta Lere mutum 4, aiki a
  gwamnatin tarayya.  kuma ya sanya an yi wa mutum  46 aikin tiyatar
  kaba tare da yi wa masu ciwon idanu aiki mutum  162.
  Har ila yau ya ce Sanatan ya dauki nauyin dalibai ‘yan wannan karamar
  hukuma 16 da suke karatun digiri a jami’o’i  har su gama karatunsu
  tare da yin wata babbar hanyar ruwa a hayin gada Saminaka da ke
  wannan karamar hukuma.
  Ya ce yanzu kuma Sanatan zai  yi babbar hanyar ruwa a sabon birni da
  garin Saminaka. Haka kuma za a ja wutar lantarki daga kwanar Narbi
  zuwa Juran kurama da Jurawa zuwa Gamagira tare da samar  injinan
  bayar da watur lantarki na taransifoma guda 5 da za a sanya a garuruwa
  daban-daban na karamar hukumar tare da aikin rijiyoyin tuka-tuka a
  garuruwan Kayarda, Tasha da Dokar Lere da Mariri da ke wannan karamar
  hukuma.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here