Sarkin Birnin Gwari Ya Koka Wa Gwamnatin Jihar Kaduna Kan Yankinsu

0
812

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MAI martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari na biyu, ya bayyana batun babu a matsayin abin da ya yi wa yankin masarautar katutu.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a gaban Gwamnan Jihar Kaduna a ranar babbar sallah.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmad El-Rufa\’i ya kai ziyarar ne inda ya yi sallar Juma\’a a can.
Mai Gwari dai ya fayyace komai kamar haka inda ya tabbatar wa kowa kuru-kuru cewa suna da matsalar tsaro domin ana satar mutane, fashi da sauran su, kuma ya ce ba su da makaranta wato babbar jami\’a ko makarantar gaba da sakandare kuma wani babban al\’amarin ma shi ne Dam dinsu da suke shan ruwa ya lalace.
\”Don haka babu shakka muna neman dauki a game da lamarin\”inji Mai Gwari.
Da yake mayar da jawabinsa,  Malam Nasiru El-Rufa\’i cewa ya yi gwamnati na nan tana kokarin warware dukkan wadannan matsaloli da cewa batun Dam za a sake gina wani ne a kusa da wancan da ya lalace.
An kuma ji El\’rufa\’i na cewa a maganar aiwatar da aiki ba gudu ba ja da baya domin za su ci gaba ne kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here