‘YAN SANDAN RIBAS SUN KAMA GAWURTACCEN DAN FASHI

0
785

MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba

JAMI’AN ‘yan sanda a Jihar Riba a wani samame da suka kai wa maboyar

gungun wasu ‘yan fashi da makami da kuma kama mutane ana garkuwa

da su domin neman kudin fansa sun yi katarin cafko wani gawurtaccen dan

fashi da kuma cin naman mutane matsayin kalaci mai suna Roland .Peter.

Dan fashin  Peter , halayyarsa ita ce idan ya kashe mutum yana datse

masa kai kana kuma ya cire masa hanta da kayan ciki, da su ne yake yin

farfesu yana ci kamar yadda ‘yan sandan suka ce ya sanar musu yanayi

Har wa yau sun ce suna zargi yana daya daga cikin wadanda suka kama wani

Fasto mai suna Samuel Okpara, suka yi garkuwa da shi suka kuma kashe shi

suka datse kansa a yankin karamar hukumar Ahoada ta Gabas a watan jiya.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani a ofishinsa yayin da aka

gabatar musu da Roland Peter da wasu mutum 22 da aka kama, kwamishinan

‘yan sandan Jihar Ribas  Zaki Ahmed,cewa ya yi yankin ba su iya runtsawa

sauran ‘yan kungiyar su da kwamishinan ya ce an kama sun hada da Justus

da aka fi sani da suna High Tension,sun addabi yankin Ahoada da kewaye

da sata, kama mutane a yi garkuwa da su .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here