An Sami Barkewar Kwalara A Birnin Zazzau

0
743

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A wani al\’amari mai tayar da hankali da bacin rai da ya faru a cikin birnin zariya na barkewar Amai da Gudawa wanda sakamakon hakan ya yi sanadiyyar mutuwar yara biyu kuma akalla guda hamsin suka kamu da cutar.

Kamar dai yadda jami\’in kula da lafiya na karamar hukumar Zariya Aminu Ahmad Ikara ya shaida wa manema labarai cewa a yanzu haka tuni sun aika da nau\’in samfurin cutar zuwa ma\’aikatar lafiya da ke Kaduna domin a gudanar da bincike a kan cutar.

Kamar yadda Aminu Ikara ya bayyana cewa suna ta daukar kididdigar yawan yara da kuma wuraren da cutar ta barke wanda sakamakon hakan suna da jimillar yara kawai guda hamsin da suka rubuta cikin ragistarsu kuma suna nan suna ci gaba aiki domin dakile cutar tare da fadakar da jama\’a ta yadda ba za a samu bazuwar Amai da gudawar ba zuwa wasu wuraren.

A ta bakin jami\’in lafiyar ya ce an samu farkewar cutar ne a unguwar Kusfa, Tudun wada da dai wadansu wuraren duk a karamar hukumar zariya da ke Jihar Kaduna.

A ta bakin wani magidanci da ya shaida wa manema labarai cewa an samu barkewar cutar a cikin gidansa inda yara Goma suka kamu.

\”Da farko dai wani yaro na ne ya kamu a ranar hawan Daushe muna wurin kallon hawa sai aka ce mini in zo Amai da Gudawa ya barke a gidana muna nan muna kokarin yi wa yaron Karin ruwa sai wancan ya Kamu sai wannan ya Kamu da haka har cutar ta Kama yara Goma\”. Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here