An Karyata Yin Arangama Tsakanin Sojoji Da Yaran Nnamdi Kanu

0
620

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojoji  ta kasa  ta musanta wasu rahotanni da ke cewa dakarunta sun kai hari tare
da kashe mutane a garin Afaraukwu na madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB,
Nnamdi Kanu.
A sanarwar da rundunar ta fitar, ta karyata labarin da kungiyar ta IPOB take yadawa da ma
wasu hotuna na mutane da ake cewa sojojin sun harba wadanda ake yadawa a intanet,a lokacin
da sojojin suka yi wa kauyen Nnamdi Kanun dirar mikiya.
A martanin da sojojin suka yi sun ce babu wani abu makamancin haka da ya faru, illa dai wasu
tsegarun kungiyar ta fafutukar kafa kasar Biafran ne suka datse hanya ga kwambar sojojin da ke
kewaya birnin Umuahia na jihar Abia a ranar Lahadi da yamma, har ta kai da suna jifan sojojin
da duwatsu da fasassun kwalabe.
Wannan al\’amari dai ya yi sanadiyyar raunata wata mata da ke wucewa da kuma wani kofur na
sojin, in ji sanarwar sojojin.
A dalilin haka ne sojoji suka yi ta harbin iska don tarwatsa mutanen.
Sanarwar ta kuma ce: \”Muna so mu gargadi masu ta da zaune tsaye da su daina yada karya
irin wannan.\” \”Muna umartar mutane da su fita su yi sabgogin
gabansu kamar yadda suka saba, su kuma kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba
zuwa ofishin \’yan sanda.\”
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun fito na fito tsakanin \’yan Biafra da jami\’an
tsaro ba.
Ko a watan Nuwambar 2016 ma kungiyar kare hakki bil\’adama ta Amnesty International ta zargi
jami\’an tsaron Nigeria da kisan a kalla masu zanga-zangar lumana 150 a watan Agustan
2015.
Kungiyar ta ce sojojin sun yi amfani da muggan makamai wajen murkushe masu zanga-zangar da
ke neman kafa kasar Biafra
Sai dai ko a wancan lokacin rundunar sojin ta musanta zarge-zargen inda ta bayyana masu
zanga-zangar a zaman barazana ga tsaron kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here