\’YAN MASSOB SUN KAI WA \’YAN AREWA HARI A ABA MUTUM HUDU SUN MUTU

0
736
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
KURA ta lafa hankali ya kwanta a Oma Hausa Unguwar Hausawa da ke garin
Aba, jihar Abiya bayan farmaki da aka kai musu ake zato ,yan kungiyar
MASSOB ne da ke fafutukar kafa kasar Biyafara ranar talata.Hakan na
zuwa ne bayan da wata babbar kotu da ke Abuja ta bayar da umarnin a
cafko mata Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB da ke fafutukar ta
kowane hali sai an kafa kasar Biyafara sun balle daga Nijeriya.
Ranar Talata da ta gabata ce bayan sojoji da sauran jami\’an tsaro sun
kai samame garin Umuahiya, mahaifar Kanu da nufin sake kama shi su kuma
\’yan Massob suka huce haushi kan al\’ummar arewa mazauna Aba da ke
gudanar da harkokin kasuwancin su shekaru masu dimbin yawa.
A shekara ta 2000. An kai wa \’yan arewar wani kazamin hari a Oma Hausa Unguwar da
suke da kuma kasuwar albasa nan ma goman rayuka aka rasa sakamakon
kafa shari\’ar Musulunci da wasu gwamnatocin arewa suka yi a jihohin su
lamarin da a wancan lokacin gwamnatin da ta gabata ta jawo matsalolin
rashin tsaro a kasar nan . An rika bin \’yan arewa da ke gudanar da kananan sana\’o\’i suke bin
lungunan Aba suna talla aka rika yi wa kisan mummuke.
da yake yi wa wakilinmu na kudanci karin bayanin yadda aka kai musu harin na
ranar Talata, Haladu Imam wani dan kasuwa mazaunin Aba ya ce “kimanin
sama da mutum 40 aka yi wa mummunan raunuka ba za a iya tantance adadin
wadanda aka kashe ba sai anjima idan mun bincika”. Ya ci gaba da cewa
“kura ta lafa halin yanzu domin an aiko mana da jami\’an tsaro kuma
Gwamna ya kafa dokar ta baci ta tsawon kwana 3.”inji shi.
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito daga wata majiya cewa kimanin mutum hudu
ne aka kashe \’yan arewa a harin da aka kai musu na ranar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here