Sheikh Bala Lau Ya Kirayi Gwamnatin Tarayya Da Babbar Murya Kan IPOB

0
1147

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SHUGABAN Ƙungiyar Jama\’atu Izalatil Bidi\’ah wa iƙamatis-Sunnah ta tarayyar Naijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau , ya yi kira da babbar murya a kan gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki na daƙile kisan gilla da Inyamurai \’ƴan a waren Ƙasar Biyafara suke yi wa Hausawa a garin Aba da wasu garuruwan inyamurai a kudu maso yammacin Najeriya.

Shugaban ya ce zura ido \’ƴan ta\’addan suna ɗauƙar doka a hannunsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba, lura da yadda \’yan Ƙabilar Hausawa a Jos suka fara ɗaukar doka a kan wasu inyamurai waɗanda ba-su-ji ba ba su gani ba a garin Jos.

Sheikh Lau ya yi kira da a tura jami\’an tsaro su daƙile wannan ta\’addancin da \’ƴan awaren suke yi wa Hausawa, kuma su zaƙulo waɗanda suka kitsa wannan rikici domin a hukunta su kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, domin babu wanda ya fi ƙarfin gwamnati\” Inji Bala Lau\”.

Shehin Malamin ya yi kira ga matasan Arewa da su yi haƙuri kada su ɗauki doka a hannunsu, saboda tabbacin cewa wannan gwamnati mai adalci ba za ta zura wa \’ƴan ta\’adda ido suna abin da suka ga dama a ƙasa ba.

A Ƙarshe Sheikh Bala Lau,ƴa kira ga Limaman juma\’a da Malamai masu karantarwa a masallatai da sauran daiɗaikun jama\’a da su sanya \’ƴan uwa Musulman yankin Rohingya na kasar Myanmar cikin addu\’oi na musamman, kan kisan ƙare-dangi daga maguzawa masu bin addinin Buddha suke yi musu.

A yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijira kimanin 400,000 da ke rakube a Bangladesh.

Sheik Lau ya yi addu\’ar Allah ya zaunar da al\’ummar musulmi lafiya a duk inda suke a faɗin duniya, ya zaunar ƙasarmu lafiya, ya mana maganin waɗanda suke neman wargajewar ƙasar amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here