GWAMNATI TA HUKUNTA MASU YADA JITA-JITA A YANAR GIZO -ARCHIBISHOP KAIGAMA

0
628

 Isah Ahmed, Jos

AKIBISHOF na darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop-bishop na darikar katolika a Nijeriya (Archibishop) Ignatius Kaigama ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya kan ta dauki matakin hukunta wadanda suke yada jita-jita a kafofin yada labarai na yanar gizo a Nijeriya. Archibishop Ignatius Kaigama ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan hare-haren da masu fafutukar neman yankin kasar Biyafara, suka kai wa al’ummar arewa mazauna yankin Inyamurai a makon da ya gabata.

Ya ce ya  kamata gwamnatin Nijeriya ta yi wani abu kan masu yada jita-jita a kafofin yada labarai na yanar gizo. Domin wadanda ba su da tunani da halin alheri ga Nijeriya suna amfani da kafofin yada labarai na yanar gizo wajen yada  abubuwan karya da suke tayar da hankulan al’ummar kasar nan.

Ya ce muna neman ci gaban Nijeriya ne ko a arewa ko a kudu ne muna neman ci gaba ne. Amma wannan al’amari da ya faru ba abu ne da zai taimaki kasar ba.

Ya yi  kira ga al’ummar Nijeriya kan mu zauna lafiya mu yi hakuri da juna.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here