BA KOMAI YA HAIFAR DA HADIN KAN AL\’UMMAR AREWA BA A ZABEN DA AKA YI ILLA WAHALA DA KUMA JUYIN JUYA HALI..Inji Halifa Hassan Yusuf

  0
  691
  Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
  DANGANE da zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin kasar nan sama da shekaru 2 da suka gabata da har ya kai ga jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban adawa na kasar nan a wancan lokacin wato janar Muhammadu Buhari ta kai ga lashe zaben tare da kayar da dan takarar jam’iyya mai mulkin kasar nan a wancan lokacin wato jam\’iyyar PDP tsohon shugaban kasa mai ci Goodluck Ebele Jonathan kan haka a kwanakin baya wakilinmu Muhammad Sani Chinade  ya  samu tattaunawa da Galadiman Damaturu kuma tsohon dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin rusasshiyar jam’iyyar PRP Halifa Hassan Yusuf yadda dattijan ya ce ba komai ya haifar da hadin kan al’ummar arewa  ba a wancan lokacin har ya kai su ga nasara illa wahala da su ka gani muraran da kuma uwa uba juyin juya hali da ya faru a kasar nan kamar yadda dama can ake hasashen zai faru, Asha karatu lafiya..
  TAMBAYA.. Me za ka ce dangane da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 2015 har ya kai ga jam’iyyar adawa a wancan lokacin karkashin janar Buhari ta kai ga samun nasarar lashe zaben?
  AMSA..To Alhamdulillahi ni dai a matsayi na na tsohon dan siyasa da aka dama da ni tun a jumhuriya ta farko kama ya zuwa jumhuriya ta biyu da kuma jumhuriya ta uku da ta hudu dama wadda mu ke ciki a yanzu duk da cewar a yanzun na dan ja baya kadan don barin sababbin yankan rake a gaskiya na san cewar wannan cin zabe da janar Muhammadu Buhari ya yi lamari ne daga Allah SWT sakamakon wassu dalilai.
  Na farko dai shine kasar nan an wahala matuka, kuma ana tsammanin Buhari zai iya ceton kasar nan da al’ummomin cikinta kasancewar a baya ya yi mutane sun gani duk da cewar lokacin mulkin sojoji ne, kuma a wannan zabe da aka yi na shugaban kasa mu mambobin jam’iyyar APC a zahiri yawanmu ko kusa bai kai yawan jama’ar da suka kada mata kuri’a ba amma cikin ikon Allah saboda tunanin cewar dan takarar da ya tsaya wa jam’iyyar wato janar Buhari mutum ne mai ruhin adalci shi ya sa kwai da kwarkwata daga kowane jinsi kasa aka kada ma Sa kuri’a ba tare da la’akari da yare ko addini ko kuma yankin da ya fito ba har ya kai ga nasara.
  Kuma abin ban sha’awa a lokacin da dan takarar ke yakin neman zabe saboda kauna da sanin halayyarsa da kuma cewar ba mutum ne da ke da kudi ba har wata tsohuwa daga jahar Kebbi ta ba shi Naira Miliyan guda
  a matsayin gudummawarta don tallafa ma sa yakin neman zabe ai ka ga abin sai a ce daga Allah ne.
  Don haka al’amari ne daga Allah (SWT) wannan nasara ta jam’iyyar APC da kuma shi kansa shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, don haka ne ma na ke kiran ‘yan jam’iyyar ta APC da kar su ci gaba da nade
  hannuwansu suce ai shike nan aiki ya kare su bar janar din shi kadai ina ai yanzu ne ma aka fara domin kuwa akwai bukatar da su yi iya kokarin su dama sauran al’ummar kasa don ganin janar din ya samu
  mashawarta nagari ba baragurbi ba da za su tallafa ma sa don hannu daya ba ya daukar jinka ta haka ne zai samu gudanar da ayyukan da suka dace ga al’ummar kasa don bambanta da mahukuntan jam’iyyar da ta bar mulki sama da shekaru biyu wato jam\’iyyar PDP ta adawa ayanzu.
  TAMBAYA.. A baya kafin gudanar da zaben 2015 ka  taba cewar, ai lalle zaben da za a yi jam’iyyar adawa za ta iya kafa gwamnati karkashin Janar Buhari,ko me ya ja hankalinka a wancan lokacin da har  ka yi wannan hasashe da ya tabbata gaskiya?
  AMSA..To a gaskiya ba komai ya sa na yi wancan hasashe ba illa sai don na san siyasar kasar nan kwarai matuka kamar yunwar ciki na kasancewar da ni aka yanke cibiyarta tun fil azal, kuma na ga babu abin da zai hada kan mu mu mutanen arewa illa wahala domin ina daga cikin dattawan da suka rika kokarin hada kan al’ummar arewa  sau da yawa don ganin an gudu tare an kuma tsira tare amma lamarin ya ci tura to amma da yake an ce jiki magayi kamar yadda janar Buhari ke fada kullum kaga ai wahala ta sa mun hada kanmu har kuma mu ka kai ga cimma burinmu na cin zabe ta hanyar maja da ‘yan uwanmu wasu al’ummar kasa.
  Don haka wahala ita ce silar hada kan mu har mu ka kai ga nasara don a sani na da na yi na kasar nan daga jumhuriya ta daya ya zuwa jumhuriya ta biyu da ta uku da kuma ta hudu shine da na buga kasar siyasa na gani sai na hango cewar, lalle a wancan lokacin jam’iyyar PDP za ta sha kasa daga hannun jam’iyyar adawa ta APC. Don haka babu abin da ya faru a kasar nan illa juyin juya hali wato (Revolution) a turance da talaka wa suka taru suka yi don ceto kasa ta yadda suka kwaci kansu daga hannun mulkin da ya yi kama da na jari
  hujja alhalin an fake da cewar mulkin dimokuradiyya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here