Fasinjoji Sun Koka Da Tsaikon Jirgin Kasa A Tasoshinsa

0
718

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

WADANSU gungun fasinjojin jirgin kasa da ke jigila tsakanin Kaduna da Abuja sun koka a kan yadda sakaci ke haifar da samun matsalar jirgin da ta haifar masu da tsayawa a wurare biyu kafin a kawo tashar da ya kamata su tsaya.

Jirgin dai ya taso ne daga Abuja amma ya tsaya a Idu sannan kuma ya kara tsayawa a Jere har na tsawon mintuna 20 lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin fasinjojin da suke ganin ana neman jefa su cikin hadarin tsaro musamman kasancewar irin yadda yankin ke fama da matsalar tsaro.

A bisa haka ne ya sa fasinjojin ke korafi tare da yin kira ga gwamnatin tarayya kasancewarta na mai alhakin tafiyar da wannan jirgin da su hanzarta daukar mataki domin kada lamarin ya zama wani abu daban nan gaba ta fuskar lafiya da dukiyar jama\’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here