Gazawar Gwamnatin Jihar Kaduna Ya Sa Likitoci Sun Shiga Yajin Aikin Sai baba tagani

0
629

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR likitoci na asibitocin gwamnatin
jihar Kaduna sun shiga yajin aikin sai-baba-
ta-gani.
Shugaban kungiyar likitocin Joseph Jokshan
ne ya sanar da haka ga manema labarai inda ya
ce sun shiga yajin aikin ne saboda irin halin
da asibitocin jihar ke ciki.
Ya Kara da cewa bayan rashin inganta aikin
likita da gwamnatin jihar ta ki yi, asibitocin
jihar duk sun lalace, inda wasu ma ba za a
iya aiki a cikin su ba.
Joseph ya kum bayyana cewa, tun farko
karfin hali kawai su key i wajen gudanar da
ayyukan su, amma a yanzu lamarin ya kai
Intaha.
Shugaban ya kuma koka da rashin
kayayyakin aiki a asibitocin da kuma rashin
ma’aikata.
A karshe ya roki jama’ar jihar Kaduna su yi
hakuri da wannan mataki da su ka dauka,
cewa hakan ya zama dole ne, kuma yana
rokon su da su mara masu baya domin kai wa ga samun nasara.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here