Takaddama Ta Kaure Tsakanin Karamin Ministan Mai Da GMD NNPC A Kan Kwangilar Dala Biliyan 20

0
641

Rabo Haladu Daga Kaduna

TAKADDAMA ta kaure tsakanin Karamin Ministan
Albakatun Man Najeriya Ibe Kachikwu da
Shugaban Kamfanin Mai na (NNPC) Mai
Kanti Baru.
A wata wasikar da ministan ya aika wa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministan
ya zargi shugaban kamfanin da \”yin ba daidai ba
da kuma rashin da\’a.\”
A cikin wasikar da aka kwarmata ga jaridun
Najeriya, ministan ya zargi Shugaban NNPC, Mai
Kanti Baru da daukar manyan ma\’aikatan
kamfanin man da kuma ba da kwagilolin da suka
haura dala biliyan 20.
\”Sabanin yadda doka ta bukata wato sai ya nemi
yardar karamin ministan,\” wanda shi ne
shugaban hukumar da ke sa ido kan NNPC.
Hakazalika ministan ya ce \”da na nemi sanin
abin da ya sa shugaban NNPC din yin hakan, sai
ya gaya mishi cewa shugaban kasan ne ya
amince da daukar ayyukan da kuma ba da
kwagilolin.
Kodayake majalisar dattawan  ta kafa
wani kwamitin bincike da zai binciki zarge-
zargen da ministan ya yi a cikin wasikar.
Takaddama tsakanin jami\’an gwamnatin Buhari
ba sabon abu ba ne.
A baya an taba samun takkadama tsakanin
Ministan Shari\’ar Abubakar Malami da
kuma Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC
Ibrahim Magu, sai dai dukkansu sun musanta
zargin.
Hakazalika, an taba samun takaddama tsakanin
Ministan Lafiya da kuma shugaban hukumar
NHIS, wadda sai da ta kai ga dakatar da
shugaban hukumar da kuma kafa kwamitin
bincike kan al\’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here