An Sami Barkewar Annobar Kyandar Biri A Jihar Bayelsa

0
708

Rabo Haladu Daga Kaduna

AN sami labarin barkewar annobar cutar kyandar Biri a Jihar Bayelsa.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar da afkuwar barkewar annobar cutar Biri a jihar
Bayelsa, kuma ta ce an kebe kimanin mutane goma da suka kamu da cutar ana ci gaba da neman wasu da dama da ake kyautata zaton sun kamu da wannan cuta domin a killace su wuri daya.
Hukumar kula da lafiya ta jihar ta aika da amfarin kwayar cutar ga sashin bincike da gwaje-gwaje na hukumar lafiya ta duniya dake kasar Senegal domin tantancewa yayin da sakamakon gwajin zai tabbatar ko annoba ce.
Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin mutane goma da suka kamu da cutar likita ne, kuma yanzu haka ana neman mutane arba’in da tara domin a kebe su, wasu rahotanni kuma sun bayyana cewa akalla mutane goma sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon kamuwa da cutar.
Mista Daniel Maxing, shi ne kwamishinan ma’aikatar watsa labaru a jihar ta Bayelsa, ya sami zantawa da manema labarai inda ya ce akalla mutane goma na kebe a yanzu haka domin kaucewa yaduwar cutar.
Jama’a da dama a fadin jihar sun bayyana halin da ake ciki a matsayin masifar da ta shafi kowa da kuma yin kira ga gwamnati da ta gaggauta shawo kan lamarin. A halin da ake ciki dai jama’a da dama ba sa musabaha da juna kamar yadda aka saba domin guje wa kamuwa da wannan cuta.
Cutar kyandar Biri dai ta samo asali ne daga Birai da kuma sauran dabbobi da ake mu’amulla da su irin su barewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here