Malaman Makaranta Fiye Da 500 Aka Kashe Sanadiyyar Rikicin Boko Haram A Jihar Borno

0
589

Rabo Haladu Daga Kaduna

YAYIN bikin ranar malaman makaranta ta duniya da aka yi a jihar Borno gwamnatin
jihar ta sanar  da cewa tayi hasarar malamanta fiye da dari biyar a shekaru shidan da aka yi ana fama da rikicin Boko Haram.

Yayin da ake bikin “Ranar Malaman Makaranta ta Duniya” jiya 5 ga watan Oktoba, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ta kowace shekara don tunawa da karrama malamai, gwamnatin Jihar Borno  ta yi kira a kan kungiyoyi masu zaman kansu da su ci gaba da dafa wa harkokin ilimi a jihar da yanzu haka ke tangarari sakamakon illar da Boko Haram ta yi wa sha’anin ilimi a jihar, abin da ya janyo mutuwar malamai fiye da 500 da aka kashe.
A cewar mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Usman Durkwa, gwamnatin jihar ta dukufa wajen inganta harkokin ilimin zamani a jihar tare da biyan bukatun malamanta duk da matsalolin da jihar ke fuskanta.
Alhaji Durkwa ya tunashe da jama’a irin matsalolin da kungiyar Boko Haram ta haifarwa jihar ta fannin
ilimi inda har ya kusa durkushewa baki daya. Sai dai yace gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen inganta ilimi.
Gwamnatin jihar ta dukufa wajen gyaran duk makarantun jihar da suka lalace musamman wadanda aka sake kwatowa daga hannun ‘yan Boko Haram a wuraren da suka mamaye a da can.
Shi ma kwamishanan ilimin jihar, Musa Inuwa Kufo ya sanar cewa gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya
saki kudin biyan hukumomin jarabawar kare karatun sakandare irinsu WAEC da NECO domin a sako wa daliban da suka kammala karatunsu sakamakon jarabawar da suka dauka.
Shugaban kungiyar Malaman jihar ya bayyana farin cikinsu tare da kuma abubuwan da suke ci masu tuwo a kwarya, inda ya bada misali da rashin biyansu kudin karin girma da na alawus-alawus da kuma samar musu ingantattun kayan aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here