Kwamishina Ringim Ya Gargadi Iyayen Yara

0
787

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

A Jihar Kuros Riba Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hafiz Muhammad Inuwa ya gargadi iyayen yara da su  rika sa ido sosai  tare da rika  jan kunnen ‘ya’yansu domin kada su rikide su zama bata-gari musamman yadda ake yawan samun gurbacewar tarbiya da ake zargin matasa da yi. Hafiz Ringim ya yi wannan gargadi ne a ganawar da ya yi da manema labarai a lokacin da ya  gabatar musu da rikakkun ‘yan fashi da makami da aka kama aka kai su ofishinsa.

Ya ci gaba da cewa, “gargadin da zan yi wa iyayen yara a jihar nan da su rika kula da takun ‘ya’yansu su san su waye abokansu da kuma irin abebadan da suke shigo musu  gida da abubuwan da ba su ne iyayen suka ba su ba su rika tambayar su. Har wa yau su daina barin ‘ya’ya sakaka kamar dabbobi”.  Ya kara da cewa “rundunata ba za ta bari duk wani bata-gari ko dan ta’adda ya ci karensa babu babbaka a Jihar Kuros Riba ba “.

Akalla mutum goma sha bakwai aka nuna wa ‘yan jarida da aka kama ake zargin su da aikata miyagun laifuka daban-daban da suka hada da kama mutane ana garkuwa da su da kuma fashi da makami a wurare daban-daban ciki da wajen birnin Kalaba.”an kama su wasun su da kananan bindigogi ,kayan tsubbu, da kananan bindigogi kirar gida da harsasai. Ya ce kotu za a mika su da zarar an gama binciken su.

Iyamba Iyamba wani daga cikin wadanda ake zargi da fashi da makami ya shaida wa wakilinmu cewa “ni ba fashi na yi ba daga na tona wa wani jami’in tsaro asiri ne yana fataucin kwayoyi yana sayarwa ne ya ce sai na ga abin da zai yi mini, shi ya sa aka kawo ni nan aka hada da ‘yan fashi”inji shi. Cikin kayan da barayin ake zargi sun sato sun hada da manyan akwatunan talbijin da wayoyin hannu

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here