Gidauniyar Bill da Melinda Gates Za Ta Taimaka Wa Jihar Neja Kan Bunkusa Harkokin Kiwon Lafiya

0
612

Rabo Haladu, Daga Kaduna

Gwamnan jihar Neja  Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana jin dadinsa ga Gidauniyar Bill da Melinda Gates a kan tallafin taimaka wa Jihar Neja wajen horas da ma’aikatan kiwon lafiya wadanda za su
dinga aiki a kananan assibitoci da ke cikin karkara domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a jihar
Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta kasar Amurka za ta taimaka wa jihar Neja kan bunkasa kiwon lafiya a jihar a matakin farko.
Gidauniyar zata horas da jami’an kiwon lafiya da za su dinga aiki a asibitocin yankunan karkara.
Shugaban Gidauniyar, Dokta Chris Elias, ya jadadda muhimmancin maida hankali a kan kiyon lafiyar al’umma a kodayaushe, kuma wannan shi ne aka fi bai wa muhimmanci a yarjejeniyar tasu da gwamnatin jihar Neja.
A karin hasken da ya ba da, Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya ce da farko za su horas da ma’aikatan
kananan asibitoci. Ya ce a shekarar farko gwamnatin jihar za ta biya kashi ishirin na kudin horas da ma’aikatan, gidauniyar kuma ta biya sauran kashi tamanin, yayin da a shekara ta biyu jihar za ta biya kashi talatin. Gwamnan ya ce haka za su dinga yi har komi ya dawo hannun gwamnatin.
Daga karshe tawagar gidauniyar da ta gwamnan jihar da ta ministan kiwon lafiyar Najeriya, Farfesa Isaac Adewale, sun isa kauyen Fuka inda aka samu bullar cutar zazzabin masassharar Lassa a kwanakin baya domin bude wani asibitin da gwamnatin tarayya ta gina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here