Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Sanarwar Bullar Masassarar Birai A Jihohi 7

0
615

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN tarayya ta ce yanzu haka akwai rahoton bullar cutar masassarar birai ko monkey pox a jihohi 7,  inda mutane 31 suka kamu da cutar.
Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa tana daukan matakan magance bazuwar cutar cikin gaggawa tare da kira ga jama\’a su guji cin naman birai da na sauran namun daji.
A wata sanarwa da cibiyar dake kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya ta fitar ta hannun babban daraktan Dokta Chukwe, na cewa jihohin da wannan cuta ta bula sun hada da jihar Bayelsa, Rivers, Ekiti, Akwa Ibom, Lagos, Ogun da Cros river, koda shike gwamnatin jihar Ogun ta musanta bullar cutar a yankin ta.
Rohotanni sun bayyana cewa akalla akwai mutane 31, da ake kyautata zaton kawo yanzu sun kamu da
wannan cuta ta masassarar Birai, kokuma sun nuna alamun kamuwa da ita.
Dokta Muslihu Kolawole, ya bayyana cewa ana samun cutar daga jikin Biri ne, wato masu cin naman Biri ko hulda da shi za su iya kamuwa da wannan cuta, haka kuma idan dan’adam ya kamu da cutar yana iya yada ta ga sauran jama’a. Cutar kan dauki tsawon makwanni biyu afin ta bayyana a jikin bil’adama.
Daga cikin hanyoyin kare kai daga kamuwa da wannan cuta sun hada da tsaftace muhalli, wanke hannu a duk lokacin da aka shiga bayan gida da kauce wa cin naman Biri da sauran namun daji da mu’amula da Birai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here