Shugaban Kasa Muhammad Buhari Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Sojoji Cikin Sirri

0
616

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN kasa  Muhammad Buhari ya gana da manyan hafsohin soji cikin sirri   manyan shugabannin ‘yan sanda da kuma mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, abun da masana suka ce yin hakan na kan
ka’ida domin lamuran tsaro.
Shugaban kasar Muhammad Buhari ya gana da manyan hafsoshin sojojin a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja.
Sun kwashe sa’o’i hudu suna ganawa amma daga karshe ba’a bayyanawa ‘yan jarida makasudin taron ba.
To sai dai masana irinsu Farfesa Muhammad Tukur Baba na ganin ganawar na da tasiri ga sha’anin tsaron
kasa. Yana mai cewa wajibi ne ma shugaban ya dinga ganawa da jami’an tsaro kowane mako saboda irin
yanayin da kasar ke ciki. Shi kuwa Aliko El-Rashid Haroun, wani tsohon hafsa a rundunar tsaron Najeriya, cewa yake akwai matsaloli da dama kamar ‘yan IPOB masu rajin neman kafa kasar Biafra da ke bukatar
a rinka maida hankali a kansu, ga kuma matsalar masu garkuwa da mutane.
Shi ma Air Commodore Baba Gamawa ya ce irin wannan ganawar ta shugabannin ma’aikatun tsaro ba wani sabon abu ba ne. A cewarsa, daga lokaci zuwa lokaci ya kamata shugaban kasa ya dinga zama da jagororin tsaro don a rinka nazarin ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da ake fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here