Ba Ruwana Da Kowace Jam\’iyya – Obasanjo

  0
  738

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  TSOHON shugaban kasa  Cif Olusegun Obasanjo ya ce ya daina shiga dumu-dumu
  harkar duk wata jam\’iyyar siyasa a kasar nan.
  Cif Obasanjo ya shaida wa manema labarai hakan ne jim kadan bayan ganawa da shugaban
  jam\’iyyar PDP Sanata Ahmed Markafi da suka ziyarce shi a Abeokuta.
  Tsohon shugaban kasar ya ce babban abun da ya sa a gaba yanzu shi ne ganin yadda Najeriya
  za ta ci gaba yana mai cewa: \”batun ci gaban Najeriya mutu ka raba ne\”.
  Ya kara da cewa Najeriya tana bukatar babbar jam\’iyya mai mulki da kuma babbar jam\’iyyar
  adawa da za ta rika sa ido kan yadda gwamnati ke tafiya don ci gaban dimouradiyya.
  Da yake tsokaci game da ganawarsa da shugabannin Jam\’iyyar PDP da suka ziyarce shi, Cif Obasanjo ya ce ya shaida wa Sanata Makarfi cewa a baya ya yi PDP amma yanzu shi ba ya wata jam\’iyyar inda ya jaddada cewa shi ba ya yin amai ya dawo ya lashe.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here