Jami\’an Hukumar Agajin NEMA Sun Fara Yajin Aiki

0
678

Rabo Haladu Daga Kaduna

MA\’AIKATAN hukumar bada agajin jin-kai ta Najeriya sun koka akan rashin biya masu
bukataunsu da gwamnati ta yi. Jami’an hukumar agajin gaggawa ta NEMA sun fara yajin
aikin gargadi na wuni uku da kuma neman shugaban hukumar Injiniya Mustapha Mai Jaja ya yi murabus.
A yau Alhamis jami’an sun yi wani gangami a gaban shelkwatar hukumar da ke birnin tarayya Abuja, dauke da kwalayen bukatar a sauke Injiniya Mai Haja daga mukaminsa, ba ma a kan batun matsin lambar cimma muradan alawus da kayan aiki ga jami’an ba.
A nasa bangaren Injiniya Mai Haj ya ce tirjiyar ma’aikatan ta zo da ban mamaki. Ya ce gwamnati ta sanya wa wasu bukatun ma’aikatan hannu wasu kuma sai nan gaba.
Mai Haja yayi kira ga ma’aikatan akan su koma bakin aikinsu saboda dole ne a bi ka’idodin gwamnati kafin a biya masu bukatunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here