Al\’umnar Jihar Kaduna Sun Koka Da Rashin Ingancin Aikin Kamfanin H  &  M

0
834

Rabo Haladu Daga Kaduna

AL\’UMMA R yankin baifas da ke Jihar Kaduna sun koka game da rashin inganci da nagartar aikin da kamfanin  H  &   M  suka gudanar na faci-facin titin hanyar baifas zuwa Abuja da suka gudanar a watannin baya da suka wuce.
A cewar al\’ummar yankin sun ce gwamnati ta yi ganganci kuma bai kamata ta ba wa karamin kamfani irin   H & M aikin baban titi mai dauke da kusan dukkanin matafiyan kasar nan ba, a cewar Alhaji Amadu Dauda gwamnati ta yi asarar kudin da ta ba wa wannan kamfani domin dai aikin ya zama tamkar ba a yi ba duk faci-facin da aka yi ya hake har ma gara da ba a yi ba.
Hanyar baifas watau titin Kaduna zuwa Abuja ya zama wani tarkwan mutuwa ga direbobi da fasinjoji da ke bin hanyar.
Kamfanin   H  &   M bahi da kayayyakin aikin da ya kamata a ba shi wannan babbar hanya mai matsala wadda ta harhake.
A karshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da su rinka hattara wajen ba da kwangiloli saboda kwalliya ta biya kudin sabulu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here