\”Dole Buhari Ya Kama AbdulRasheed Maina\”

0
679

Rabo Haladu Daga Kaduna

MASU fafutuka a Najeriya sun ce ya zama wajibi shugaban Muhammadu Buhari ya kama tsohon
shugaban kwamitin yin garambawul ga tsarin fanshon kasa AbdulRasheed Maina, in har da
gaske yake yaki da cin hanci da rashawa.
Shugaban kwamitin da ke bai wa Shugaba Buhari shawara kan yaki da cin hanci da rashawa,
Farfesa Itse Sagay, yana sahun gaban cikin masu kira ga shugaban kasa  ya sa a kama
tare da hukunta AbdulRasheed Maina.
Farfesa Sagay ya ce ya kamata a hukunta duk wanda yake da hannu a mayar da AbdulRasheed
Maina bakin aiki domin su ma sun taimaka wajen aikata laifi.
Baya ga Farfesa Itsey Sagay, fitaccen lauyan nan, Femi Falana, shi ma ya fito ya ce dole a
kama AbdulRasheed Maina domin ya amsa tuhume-tuhumen da hukumar EFCC take masa.
Ya kuma ce ya zama wajibi a hukunta dukkan masu hannu a mayar da Maina aiki domin suna
neman su hana ruwa gudu ne a yakin da shugaban kasa ke yi da cin hanci da rashawa.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya
ce: \”Ana mayar da wanda ake tuhuma da satar biliyoyin nairori bakin aiki, kuma kuna tunanin
Buhari yana yaki da cin hanci da rashawa.\”
Wasu da aka sani da goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari da ke da mabiya a shafukan
sada zumunta irin su Omojuwa ma, sun yi tir da mayar da Abdulrasheed Maina bakin aiki.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Omojuwa ya ce wannan abin kunya ne ga
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta fara
neman Abdulrasheed Maina ruwa-a-jallo ne a shekarar 2015 kan zargin yin sama da fadi da
Naira Biliyan biyu cikin kudin yin garam bawul wa tsarin fanshon Najeriya.
A wancan lokacin har zanga-zanga wasu suka yi zuwa majalisar dokokin  domin nuna
goyona baya ga Abdulrasheed Maina. Amma bai fito ya kalubalanci neman da ake yi masa ba.
Bayan EFCC ta yi shelar nemansa ne aka daina jin duriyar Abdulrasheed Maina.
Ba a sake jin labarinsa ba sai lokacin da rahotanni suka ce ya koma aiki a ma\’aikatar
cikin gida ta Najeriya, a matsayin daraktan riko.
Amman ministan ma\’aikatar cikin gidan, Abdulrahman Dambazau, ya ce shi bai san komai
ba dangane da dawowar AbdulRasheed Maina aiki.
Wata sanarwa da sakataren yada labaran ministan, Ehisienmen Osaigbovo, ya fitar ta ce
daga ofishin shugaban ma\’aikatan
aka turo Abdulrasheed aiki a ma\’aikatar.
Saboda haka ministan bai san yaya aka yi Abdulrasheed Maina ya dawo ma\’aikatarsa ba.
Mai magana yawun hukumar EFCC ya tabbatar da cewa, har yanzu hukumar tana neman
AbdulRasheed Maina, ruwa-a-jallo.
Bugu da kari, sanarwar da hukumar EFCC ta bayar cewar tana neman Maina har yanzu tana
nan a shafinta na Intanet.
Kawo yanzu dai gwamnatin Shugaba Buhari ba ta fitar da wata sanarwa da dangane da komawa
aikin gwamnatin da AbdulRasheed Maina ya yi ba a lokacin da hukumar EFCC take namansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here