HANA LIKITOCI AIKI A ASIBITOCI MASU ZAMAN KANSU YA YI DAIDAI-DOKTA BANINGE

0
627

 Isah Ahmed, Jos

WANI fitaccen mai maganin gargajiya da ke zaune a garin Jos babban birnin Jihar Filato, kuma Sarkin maganin kasar Ningi da ke Jihar Bauchi Dokta Ibrahim Baninge ya bayyana cewa yunkurin da gwamnatin tarayya take yi, na hana likitoci da suke aiki a asibitocin gwamnati  aiki a asibitoci masu zaman kansu, ya yi daidai. Dokta Ibrahim Baninge ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce wnannan mataki na hana likitocin gwamnati aiki a asibitoci masu zaman kansu ya yi daidai, domin sakamakon  rashin daukar wannan mataki ne ya sanya likitocin da suke aiki a asibitocin gwamnati, suke yi wa asibitocin makarkashiya.

Ya ce idan ba don makarkashiyar da likitocin suke yi ba, babu yadda za a yi a kowanne lokaci su tafi yajin aiki, kuma babu yadda za a yi a je manyan asibitocin koyarwa na kasar nan, a rasa kayayyakin aiki.  Don haka wannan yunkuri na daukar wannan mataki  yi daidai.

‘’Babu shakka wannan abu zai taimaka wajen bunkasa ayyukan asibitocin gwamnati a kasar nan, domin idan ma’aikatan asibitocin gwamnati  suka hada kansu waje daya, dole ne aiki ya tafi daidai. Muna kira ga likitoci su yi hakuri su rungumi wannan mataki da gwamnati take kokarin dauka’’.

Daga nan ya yi kira ga gwamnati ta daukaka maganar kiwon lafiya  da harkokin ilmi a Nijeriya. Ya ce  idan gwamnati ta yi haka ta gama komai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here