\’YAN BINDIGA SUN BINDIGE \’YAN SANDA 2 KUMA SUN YI GARKUWA DA BATURE A KOGI

0
654
Daga Usman Nasidi
HUKUMAR \’\’yan sandan Jihar Kogi ta tabbatar da bindige jami’anta guda biyu a hannun wasu \’yan bindiga da suka kai musu hari, sa’annan suka yi awon gaba da wani Bature dan kasar Fotugal.
Kakakin rundunar, William Aya ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Lakwaja, inda ya ce \’yan sandan da aka kashe sun hada da Insfekta Ezekiel Negedu da kuma Sajan Gini John.
\’Yan sandan sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke gadi a kan titin Obajana – Oshokoshoko – Kabba, inda ya ce John ya mutu nan take, yayin da Negedu ya mutu bayan an garzaya da shi asibiti.
\’Yan bindigan sun kai su goma sha biyar, kuma sun fito ne daga wani daji, inda suka far wa \’yan sandan da ke gadin ma’aikatan da ke gudanar da aikin titin Obajana, inda suka tafi da Jose Machada dan kasar Fotugal.
Daga karshe Kakakin ya ce kwamishinan \’yan sandan jihar, Ali Janga ya tura jami’an tsaro na musamman don raka \’yan bindigan da nufin kamo su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here