Muna Goyon Bayan Fayose – Gombe

  0
  811

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  MALAM Musa Tukur Gombe shugaban kungiyar matasan Arewacin Nijeriya ne da ke fafutukar ganin gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya zama shugaban tarayyar Nijeriya.

  Musa Tukur Gombe ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa suna wannan fafutukar ne ganin irin yadda Fayose yake fadin abin da ke zuciyarsa wanda za a Iya cewa dai dai ko sabanin hakan.

  \”Mu a cikin Gwamnatin Buhari babu matasa musamman cikin ministocinsa duk masu yawan shekaru ne don haka kasancewar matasa ne mafi yawan masu jefa kuri\’a matasa ne dole a yi da matasa\”

  Gombe ya ci gaba da cewa ana maganar kasa baki daya ne don haka muka \”na kafa kuma Ina shugabantar wannan kungiya ta matasan Nijeriya daga arewa domin ganin Fayose ya samu nasarar da ake bukata ta yadda kasar za ta ci gaba da zama daya al\’umma daya\”.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here