WADANDA SUKA AMFANA DA ZABEN SAK SUN CI AMANAR GWAMNATIN BUHARI-MURTALA MAMSA  

0
696

Isah Ahmed, Jos 

MALAM Murtala Abdullahi Musa [Mamsa] da ke zaune a garin Mista Ali da ke karamar hukumar Bassa a jihar Filato,  daya ne daga cikin mawakin shugaban kasa Muhammad Buhari. Domin ya yi wa shugaban kasa Buhari wakoki da dama tun daga  lokacin da ya fara  fitowa  takarar shugabancin kasar nan, har ya zuwa lokacin da ya sami nasara. A yanzu kuma  ya fito takarar shugabancin karamar hukumar Bassa karkashin jam’iyyar APC.  

A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa wadanda suka amfana da zaben sak da aka yi a lokacin zaben da ya gabata sun ci amanar gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari. Domin ba sa amincewa da duk wani abu da ya kawo don taimaka wa al’ummar Nijeriya.

Har’ila yau ya bayyana cewa  idan majalisun jihohin kasar nan suka ki amincewa da gyaran dokar bai wa kananan hukumomin kasar nan \’yanci da aka gabatar masu, sun nemi rigima ne da talakawan Nijeriya domin abin da suke bukata kenan.

Haka kuma ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar fitowa takara tare da kudurorinsa ga karamar hukumar Bassa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

GTK; A matsayinka na dan takarar shugabancin karamar hukuma mene ne ra’ayinka kan kokarin da ake yi na bai wa kananan hukumomin kasar nan \’yanci?

Murtala Mamsa; Ni addu’ata kan wannan magana ita ce kamar yadda aka kai wa majalisun jihohi wannan magana ina fatar za su ba ta goyan baya da hadin kai, su amince da ita. Idan ‘yan majalisun jihohin kasar nan suka ki amincewa da bai wa kananan hukumomin kasar nan \’yancinsu. To sun nemi rigima da talakawan Nijeriya.  Domin abin da talakawan Nijeriya suke nema kenan. Idan akwai dan majalisar da yake son ya sami matsala da talakawan Nijeriya, ya ki amincewa da wanann magana. Ra’ayin talakawan Nijeriya ne domin babu wani mai mulki da yake kusa da talaka, kamar shugaban karamar hukuma da kansila

Idan aka bai wa kananan hukumomin \’yanci aka sakar masu mara. Za a turo masu kudadensu kai tsaye daga tarayya. Kuma  su kansu ‘yan majalisu za su huta, domin su dama masu yin doka ne. A yanzu idan ka je gidajen ‘yan majalisa za ka sami mutane sun yi dafifi suna neman a ba su aiki ko kuma a tallafa masu. Amma idan aka bai wa kananan hukumomi \’yanci aka sakar masu mara, za su warware wadannan matsaloli na talakawa.

A yanzu shi kansa shugaban kasa ya san ana sako kudi amma ba sa zuwa ga talakawa saboda wannan matsala. A duk lokacin da aka turo kudade don a yi wa talakawa aiki sai gwamnoni su rike. Don haka wasu gwamnoni sun ki yin zabe. Suna nada shugabannin riko a kananan hukumomin jihohinsu. Don haka wasu gwamnonin sai abin da suka ga dama suke yi a jihohinsu.

Idan aka bai wa kananan hukumomin kasar nan \’yanci maganar gwamnoni su rika nada shugabannin riko a kananan hukumominsu ya kare. Misali  Idan aka bai wa kananan hukumomi \’yanci aka zabi shugaban karamar hukuma, idan aka turo masa da kudi Naira Miliyan 100, Gwamna ya cire wani abu shugaban karamar hukuma zai iya tuhumar Gwamnan. Amma idan ba a bai wa kananan hukumomi \’yanci ba, idan Gwamna ya nada shugaban riko aka turo kudi Naira Miliyan 100 ko Naira Miliyan 10 ya kawo ya bai wa shugaban karamar hukuma babu abin da zai ce, domin zai ji tsoron kada Gwamnan ya cire shi, saboda shi ne ya nada shi.

Ya kamata Gwamna ya kula da ayyukansa na jiha haka shi ma shugaban karamar hukuma ya kula da ayyukan karamar hukumarsa ba tare da wani katsalandan ba. Don haka muna goyan bayan wannan yunkuri da ake yi na bai wa kananan hukumomin kasar nan \’yanci.

Babu wani dan majalisa da ya isa ya yi adawa da  maganar  bai wa kananan hukumomi \’yanci a Nijeriya. Domin babu hujjar yin adawa da wannan magana. Saboda haka ina kira ga ‘yan majalisun jihohin kasar nan su amince da wannan doka ta bai wa kanannan hukumomi yanci kamar yadda ‘yan majalisun dattawa da ‘yan majalisun wakilai na tarayya suka amince.

GTK; To maye ya karfafa maka gwiwar fitowa wannan takara?

Murtala Mamsa; Abubuwa uku ne suka karfafa mani gwiwar fitowa wannan takara. Na farko shi ne mu ne muka yi ta tallar shugaban kasa, Muhammad Buhari da jam’iyyar APC da take kan  mulki yanzu. Amma abin kunya da takaici sai muka ga yawancin wadanda suka zo suka shiga wannan jam’iyya daga baya, manufarsu daban da ta shugaban kasa, da mu da muka yi tallarsa.

A lokacin da aka zo zaben da ya gabata, shugaban kasa yace a yi sak, kuma a duba cancanta. Amma  yau an wayi gari zaben da aka yi na sak, ya kawo matsala a wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari.  Domin  idan shugaban kasa ya kawo wani abu, wanda zai taimaki al’ummar kasar  nan, wadannan mutane da suka sami dama sakamakon zaben sak, sai suki goyan bayansa. Muna ganin wadannan mutane sun ci amanar shugaban kasa, shi ne ya sa a matsayina na masoyinsa, na fito wannan takara. Domin na mara masa baya kan manonufofinsa na tallafa wa al’ummar kasar nan.

Kuma a wannan karamar hukuma ta Bassa  dattawa sun dade suna mulki,  amma babu wani ci gaba da aka samu don  haka matasan wannan karamar hukuma suka ce na fito wannan takara.

GTK;  Mene ne kudurorinka ga wannan karamar hukuma idan Allah Ya sa ka sami nasara?

Murtala Mamsa; Kudurorina ga wannan karamar hukuma sune samar da ayyukan yi ga matasan wannan karamar hukuma, domin a baya,  ba a bai wa matasan wannan karamar hukuma aiki ba. Muna da manyan mutane a wannan karamar hukuma, amma babu wani mutum da ya bude ko da gidan kaji ko wani kamfani ko wata ma’aikata  don samar da ayyukan yi ga matasan wannan karamar hukuma.

Muna da wuraren da ake hakar kuza a wannan karamar hukuma, irin abin da matasan wannan karamar hukuma suke yi kenan. Duk da matsalolin da ke tattare da wannan aiki.

Don haka babban kudurina shi ne samar da ayyukan yi ga matasa, domin rashin aikin yi ne ya sa ake yawan samun rikice-rikice. Amma  yau idan matashi ya sami aiki ko ya sami wajen yin sana’a ko kasuwanci idan aka zo hayaniya ba zai sanya kansa a ciki ba.

GTK; Ganin irin rikice-rikicen da ake yi a wannan karamar hukuma idan Allah ya sa ka sami nasara wadanne hanyoyi ne za ka bi wajen magance wannan matsala?

Murtala Mamsa; Duk rikice-rikicen da ake samu a kasar nan musamman arewa iri daya ne. Wato  ba su wuce rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma ba. Kuma ‘yan siyasa ne suka hada kashi 70 bisa 100 na irin wadannan rikice-rikice. Don haka za mu bi duk hanyoyin da suka kamata wajen ganin an magance irin wadannan rikice-rikice a wannan karamar hukuma. Kuma za mu wayar wa da matasa kai kan muhimmancin zaman lafiya.

GTK; Ganin irin manyan mutane suka fito wannan takara karkashin jam’iyyar APC kana ganin za ka sami nasara?

Murtala Mamsa; Tsakani da Allah kamar yadda na fada matasan wannan karamar hukuma ne suka bukaci na  fito wannan takara, domin suna ganin ni ne nafi cancanta. A cikin wadanda muke wannan   takara, akwai wanda  ba a jihar nan yake zaune ba. Akwai wadanda sun yi ayyuka da dama amma ba su dauki ko mutum daya aiki  daga wannan karamar hukuma ba. Don haka da yardar Allah zan sami nasara kan wannan takara.

GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar karamar hukumar  Bassa?

Murtala Mamsa; Sakona ga al’ummar karamar hukumar Bassa shi ne mu hada kai mu so junanmu mu yi ta addu’a kuma mu manta da maganar banbancin addini da kabila a wannan zabe, mu zabi wanda ya cancanta  domin mu sami ci gaba a wannan karamar hukuma da jihar Filato da kasar nan gabaki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here