Shugaban Kasa Buhari Ya Sauke Sakataran Gwamnatin Tarayya

0
705

Rabo Haladu Da Mustapha Imrana Daga  Kaduna

Shugaban  kasa Muhammadu Buhari ya kori sakataren gwamnatin  Babachir Lawal, inda ya maye
gurbinsa da Boss Mustapha.
Shugaban kasar ya kuma kori shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambasada Ayo Oke.
Wata sanarwa da mai ba shugaban shawara kan yada labarai Femi Adesina ta ce Shugaba
Muhammadu Buhari ya amince da shawarwarin da kwamitin da ya binciki manyan jami\’an gwamnatin biyu.
\’Yan kasar sun dade suna jiran matakin da shugaban kasar zai dauka kan zarge-zarge da ake yi wa jami\’an gwamnatin da almundahana.
Tun da farko an dakatar da Babachir ne saboda zargin saba ka\’idojin ba da kwangila karkashin shirin gwamnati na raya yankin arewa maso gabas wanda Boko Haram ta daidaita. An kuma zarge shi da sama ka\’idojin aikin gwamnati.
Shi kuwa Ambassador Oke ya gamu da fushin shugaban ne bayan da hukumar EFCC ta gano
makuden kudade a wani gida a Legas.
Rahotanni sun ce hukumar NIA ta ce kudaden, kimanin Naira biliyan 13, nata ne, abin da ya haifar da rudani a kasar. Dukkan mutanen biyu dai sun musanta zarge- zargen. \’Ba bambanci tsakanin Buhari da Jonathan\’
Shugaba Buhari ya kuma amince da kafa wani kwamitin musamman mai mambobi uku don yin nazari akan ayyukan hukumar NIA.
Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai bada shawarwarin yadda za\’a inganta ayyukan hukumar tattara bayanan sirrin ta NIA.
A baya dai Jam\’iyyun adawa a Najeriya sun yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Buhari tanayin son kai.
Bayan korar jami\’an gwamnatin daga mukamansu. Jama\’a da dama za su zuro ido don ganin ko
gwamnati zata mika su ga hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa ko kuma korar ce kawai
hukuncinsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here