An Yi Dokar Hana Kiwo A Gurbataccen Yanayi – Bugaje

0
664

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

TSOHON dan majalisar dokoki ta tarayya daga jihar Katsina Dokta Usman Bugaje, ya bayyana kokarin hana kiwon dabbobin da wasu jihohin kasar ke yi da cewa wani al\’amari ne gurbatacce domin an yi dokar ne a cikin yanayin tashe-tashen hankali da matsalar batutuwan kabilanci da bambance-bambance da yawa.

Usman Bugaje ya bayyana hakan ne a cikin wata hirar da ya yi da kafar yada labarai ta muryar Amurka sashen Hausa wanda wakilinmu ya saurara a Kaduna.

Bugaje ya ci gaba da bayar da shawarar cewa ya dace mai Alfarma Sarkin Musulmi ya kira wani babban taro da shugabannin Fulani na kasa baki daya domin tattaunawa a kan matsalar dokar kiwon da wasu jihohin kasar ke yi.

\”Ta yaya za a ce kowace jiha kawai sai ta kafa doka da kanta ba tare da yin la\’akari da wasu abubuwa ba, misali idan gwamnan Ekiti Fayose ya kafa dokar kiwon, kuma Banuwai nan ma an kafa to idan bafulatani zai ta fi Jihar Inugu ta ina zai bi da dabbobinsa? Ko zai dauki dabbobin ne a kai ya tafi da su?

Ya dace a tara makiyayan nan domin tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi domin samo mafita da kuma samun hanyoyin zamani na yin kiwo ta yadda za a samu ci gaban da ake bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here